Wannan Dai Kyauta Karo na Biyu Kenan Mlm Falalu na Samun Number Yabo Da girmama A Garin Na Shinkafi, Sakamakon Kokarin Sa Akan Aikinsa da hazaka game da Baiwar Da Allah Yayi mishi,
Sakamakon Kyautar Da ya samu Yasa muka Bibiyi Wasu Ma`abota Amfani da Social Media na Garin a shafukan Su, inda muka Tarar suna taya shi murna da nuna Farin Ciki akan Wannan Gagarumar kyauta da yasamu A jiya Jumu`a ,
A inda daya Daga cikinsu Mai Suna Mas`udu Dan Masani Shinkafi yake cewa: -
Muna Taya Mlm Cinye Wannan Kyautar a Karo na Biyu, Tabbas Aikin ka da kokarin Ka, hade da Gwarzantakar ka, da kaketa Yi Badare ba rana, a bayyane ko a boye ya cancanci Kasamu wannan kyautar harma fiye da Ita,
Inda yaci gaba dayi masa Addu'a yana Fadar
Rokon mu a Wurin Allah ya kare mana kai Shugaba, Gwarzon Mu, jarumin mu, Illahy ya kara Kwazo da karfafawa, bihakki Sayyadah Zahara (sa)
Ya Karbi Kyautar Ne a Hannun Wakilin Yan Uwa Almajiran. Sherik Ibraheem Yaqub Al`zakzaky na Garin Shinkafi, Mlm Qaseem Shehu Shinkafi,
![]() |
Lokacin Da yake karbar kyautar kenan |
A lokacin bayar da kyautar wakilin Gani da Ido ya Bayyana mana Farin Cikin da Mahalarta taron Suka bayyana a lokacin da Ake mika masa kyautar a hannunshi, inda Soka Rude filin taron da Salatin Annabi tare da kabbara.
Duk da Munyi kokarin Zantawa da shi domn bayyana mana murnar sa Hakan bata samu ba saboda Kokarin Aikin dayakeyi ayau akan Shiga Kotun da akayi da su Sayeed (h).. Amma daga baya idan Muka zanta dashi zakuji yadda takaya..
Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
Tags:
Munasabobi