@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HAQQIN SHUHADAH HAQQIN DA YA ZAMA WAJIBI KAN DUKKAN 'YAN'UWA
A cigaba da zagaye kan tattara haqqin shuhadah wanda aka saba cikin kowacce shekara , wakilin 'yan'uwa na Bauchi Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ya ziyarci da'irar Ningi tare da 'yan rakiyarsa wakilan Shuhadah da suka hada da;
Mal. Isma'ila Abba Bauchi,
Mal. Sulaiman Steaker Alqaleri , da kuma
Mal. Yusuf Dahiru Bununu (wakilin 'yan'uwa na Ningi ) .
Wannan ba shine zagayen farko ba, sai dai ya kasance na qarshe don harhada adadin abinda kowacce da'ira ta taro kafin zuwan ranar Shuhadah .
Shehin malamin ya gargadi 'yan'uwa sosai wajen wajibcin sauke wannan haqqi da ya zama wajibi akan dukkan 'yan'uwa (brothers and sisters )don tallafawa 'ya'yan shahidan harka islamiyyah wacce Sayyid Zakzaky (H )ke jagoranta.
Bayan wasu adadi da aka riga aka bayar a zagayen farko, jiya lahadi 23-2-2020 an iya samar da kudi Naira dubu dari uku da sittin da dari biyar (#360,500 )cikin garin Ningi da sauran da'irorin da ke qarqashinta.
Ji da kuma ganin yadda 'yan'uwa suka taka rawar gani yasa Shehin malamin ya nuna farin cikinsa tare da jinjina ga 'yan'uwa.
Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
Cikin jinjinawar tasa yake cewa;‘’ GASKIYA WANNAN DA'IRA TA NINGI TA TAKA RAWAR DA WASU MANYAN DA'IRORI BASU TAKA BA.‘’
Kuma har yanzu akwai wasu alqaluman da ake jira daga wasu 'yan'uwa da basu gama sauke alqawuran da suka dauka ba.
ALLAH YA BAWA KOWA IKON SAUKE WANNAN HAQQI NA 'YA'YAN SHAHIDAI DA KE KANMU .
FREE
S
A
Y
Y
I
D
ZAKZAKY (H ) !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
~24th February, 2020.