An gabatar da muzaharar kiran a saki Malam [H] Jiya Jummu’a a Abuja

A Ranar Jummu’a 28 ga watan fabrairu 2020, kamar sauran makwanni da suka gabata ‘yan uwa sun ci gaba da gabatar da gangami da muzaharar lumana ta kira ga gwamnati data gaggauta sakin jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sayyid Ibrahim Zakzaky.
(ABNA24.com) A lokacin muzaharar ta jiya ‘yan uwa sun gabatar da gangami a gaban babban masallacin kasa dake Abuja inda Malam Muhammad Abbare Gombe ya gabatar da gajeren jawabi sannan aka dauki muzahara kamar yadda aka saba.

Rahotanni na nuna cewa a jiya Jummu’a jami’an tsaron sun yi wani shiri da basu saba yin irin sa ba, wanda yasa masu lura da lamurran yau da kullum suke ganin akwai wani kulli na musamman.

Sai dai rahotannin sun ci gaba da nuna cewa an yi muzaharar lafiya kuma an kammala lafiya.
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post