Allah Na Karɓar Aikin Da Aka Yi Shi Da Taƙawa Ne!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Babban dalilin da yasa Allah ya halicci mutuwa da rayuwa shine don ya jarraba mu yasan mafi kyawun aiki daga cikin mu.

Shi kuma aiki ba zai taba zama mai kyau ba har sai an kyautata/tsarkake ninya cikinsa. Ita kuma a zuciya take ba wai bayyanata ake,yi ba ballantana wani yace ya santa.

Saboda haka za ka iya samun mutane masu yawa da ke yin aikin yabo a zahiranci, amma sakamakon rashin tsarkin niyya sai aikinsu ya tashi a banza.

Wasu kuma sai ka ji har zaginsu ake yi wai cewa duk abinda suke yi ba don Allah bane, alhali masu fadin haka ba su da ikon tsaga zuciyar mai wannan aiki ballantana su yi masa hukunci na adalci .

Allah shi ke hukunta ayyukan bayi ba wani ba. Wannan dalili ma yasa Ibn Khaddab ke cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ ALLAH NA SAUKAR DA AYA KAN MUNAFUKAI A ZAMANIN ANNABI, AMMA YANZU MUNA HUKUNTA MUTUM NE BISA ABINDA YA BAYYANA  DAGA GARE SHI .‘’

Cikin wannan hadisi na Ibn Khaddab ba zai zama hujja ko ma'auni wajen hukunta ayyukan bayi ba, domin da yawa akan samu mutane masu aiki wadanda sun cancanci yabo a zahiri, amma a badini aikin nasu zai,iya zama abin zargi.

Ayyukan wasu kuma sai kaga kamar abin zargi ne ko qasqantarwa a zahiri, amma a badininsa abin yabo ne wajen Allah (  T ), domin shine mafi sanin abinda ke boye da bayyane.

Wannan hadisi na Manzon Allah ( S.A.W.W)zai fi zama madogara fiye da waccan hasashe na sama.

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

 Bukhari yace, Muhammad Bn Katheer ya bamu labari, Sufyan ya bamu labari daga A'amashu, daga baban Wa'ili, daga baban Musa yace; Wani mutum ya zo wajen Annabi (S.A.W.W ) sai yace, mutum ne da yake yaqi don qabilanci, da wanda ke yin yaqi don nuna jaruntaka , da wanda yake yi don riya, to, cikinsu wanene me yin a hanyar Allah? Sai yace;

‘’ WANDA YAYI YAQI DON KALMAR ALLAH TA KASANCE ITA CE MADAUKAKIYA, TO, SHINE MAI YI DON ALLAH .‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 7458)

Mu kuma ba mu isa hukunta ayyukan mutum ba, sai dai mu bar al'amarinsa ga wanda ya halicce shi.

Na'am, idan ta bayyana mutum na aikata abinda Allah ya hane shi, to, wannan hukuncinsa a bayyane yake.

Daga wakilanmu na  Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

    08137925034

~5th February , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post