Alhamdulillah! KOTU TA SALLAMI SAURAN YAN UWAN DA AKE TSARE DA SU TUN WAKI'AR ZARIYA

Yau wata babbar kotu a Kaduna ta wanke ragowar yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky kusan mutum 100 da ake tsare da su a kurkukun Kaduna tsawon fiye da shekaru hudu bisa zarginsu da laifin kashe Soja guda daya a yayin da sojojin Nijeriya suka kai hari gidan Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Zakzaky a ranakun 12-14 ga Disambar 2015.

A yau Alkaliyar ta karanta Hukunci, inda ta bayyana cewa yan uwa ba su aikata wani laifi ba, ba su kashe soja ba! Ba laifin da suka aikata. Don haka ta sake su.

Wannan ya tabbatar da cewa an zalunci Malam Zakzaky ne, an kuma cutar da almajiransa ne a tsawon wadannan shekarun.

Dama kuma daga tuhumar da gwamnatin Kaduna ke wa Shaikh Zakzaky a kotu har da cewa wai ana zargin shine ya ingiza wadanda ake tsare da su din wai suka kashe Soja a yayin da aka kawo masa hari a gidansa da ke Gyallesu. Yanzu ta bayyana karara cewa shari'ar Shaikh Zakzaky da tuhumar da ake masa baki daya shirme ne. Domin wadanda ake zargi da kisan kan ma ta tabbata ba su aikata ba, bare kuma wanda ake tuhuma da ingiza su.

Muna godiya ga Allah da wannan nasara. A karo kusan na 9 kenan da Harkar Musulunci, ko Islamic Movement In Nigeria, ko abin da suke kira IMN take nasara a kan Jami'an tsaro da gwamnatin Buhari a Kotuna daban daban a Kasar nan, alhali ko so daya gwamnati ba ta taba nasara a kan yan uwa Musulmi ba.

Muna muku murna ya ku ya uwa, muna Barka da dawowarku. Allah Ya tabbatar da ku da mu a tafarkin nan na Shiriya karkashin Jagorancin Sayyid Zakzaky (H).

— Saifullahi M. Kabir
21/2/2020 — 27/6/1441H
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post