A'isha Dikko: Duniya dai tana jinku, kuma tana bibiyar shirmenku da rashin imaninku a kan Malam Zakzaky (H) da Almajiransa game da sharrin da kuke yi musu ke da iyayen gidanki|


MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Kotu ta wanke Almajiran Malam Zakzaky ta ce ba su aikata abubuwan da kuka ce sun aikata ba, har ta sallamesu sun koma cikin 'yan uwansu, yanzu kuma ke da Ubanki El-rufa'i kun ce sai kun daukaka kara a babbar kotu, har kina fada a gidajen Rediyo kina cewa wai lalle 'yan uwa sun aikata laifi, da a ce ke mai hankali ce, da kin lura da cewa, ko a iya tambayoyin da dan jarida ma yake yi miki, tun daga nan za ki san cewa yau ba jiya ba ce, lalle duniya ta gaji da wannan iskancin na ku a kan Malam Zakzaky da Almajiransa, hatta 'yan jaridar da kuke amfani da su sun fara dawowa daga rakiyarku, haka ma sauran mutanen da suke yarda da karyarku, su ma sun gane cewa duk abun da kuke yi wa Malam Zakzaky (H) da Almajiransa tsantsar zalunci ne.

A karshe, ke da iyayen gidan naki, ina yi muku Albishir da cewa, yanzu ne ma kuka fara kwasar kaskanci, kuma haka za ku cigaba da kaskanta, domin ita gaskiya guda daya ce, kuma ita Allah ke goyawa baya, ba ya goyon bayan karya da makaryata, kuma Alkawarinsa ne cewa, zai taimaki duk wanda aka zalunta a kan wanda ya zalunce shi, don haka yanzu kuka fara kunyata, kuma za ku yi mafi munin kunyata duniya da lahira Insha Allahu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post