@Ma'asumah Nigerian News Update@
--------------------------------------------------
Abdullahi AlkarazubiyTsafe
Hakkin iyaye ga 'ya'yan su yana daga cikin mafi girman wajibai a Musulunci. Allah Subhanahu a cikin kur'ani mai tsarki ya gwama kyautatawa iyaye da ibada a cikin aya guda dake cikin suratul isra'i. Duba aya ta 23 zuwa aya ta 25.
قال تعالى ( وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا (٢٣) وَاخْفِضْ لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ وَقُلْ رَبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا (٢٤) رَبُّكُمْ أَعْلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمْ إِنْ تَكُونُوا صَالِحِينَ فَإِنَّهُ كَانَ لِلْأَوَّابِينَ غَفُورًا (٢٥) سورة الاسراء
Imam Sadiq (as) Jikan Manzon Allah (S) yana cewa a cikin bayanin ma'anar ''Al'Ihsaan'' cikin wannan aya cewa Ihsaani shine; ka kyautata alakarka da su (Mahaifa), kar ka yarda ka yi jinkirin biya masu wata bukata har su kai ga tambayar ka, koda sun kasance sunada wadata. Imam ya cigaba da cewa ''Yana wajaba ga mumini ya kasance a cikin mafi kolin dabi'a a cikin mu'amalar sa da iyayen sa, kuma ya yi masu abinda suke bukata kafin su tambayershi'' Ya zo a tarihi cikin littafin Attargiib wat Tarhiib 3/316 cewa wani mutum ya tambayi Annabin tsira (S) cewa miye hakkin iyaye a kan 'ya'yan su? sai Manzo (S) ya ce; Su (Uwa da Uba) Aljanar ka ne da wutar ka. Hakan kenan yana nuna makomar mutum a lahira ya dogara ne a kan alakar sa da iyayen sa.
Har wa yau akwai hadisi a cikin kanzul ummal cewa; ''Aljanna tana a karkashin iyaye ne''
To, ashe kenan idan dai hadafin mu shine shiga aljanna a lahira? to dole mu zama masu tsantsar Tawadu'u da biyayya ga iyayen mu indai ba a kan sabawa Allah bane, domin aljanna tana a karkashin kafafun su, kuma kyautata masu shine hanyar da zata kai mu zuwa aljanna.
Akwai Hadisai birjik da ke magana a kan nisantar sabawa iyaye, zamu takaitu da daya ko biyu. A cikin Kanzul ummal Manzon Allah (S) yana cewa; Ana cewa mai gujewa (saɓawa) iyaye ''Aikata duk abinda ka so, hakika ni (Allah) ba zan gafarta maka ba'' Kazul Ummaal H 25527.
Sannan ya zo a cikin Biharul anwar 84/61 Imam Sadiq jikan Manzon Allah (S) Yace; ''Duk wanda ya kalli iyayen sa irin kallo na wanda yake fushi da su matsanancin fushi saboda sun zalunceshi to Allah ba zai karbi sallar sa ba'' Kenan koda mahaifan ka sun yimaka wani abu da za'a iya auna shi a ma'aunin cewa sun zalunceka to a nan hakuri ne ya kamaceka, idan kuwa ka yi fushi da su a kan haka, to akwai matsala! Don kuwa sallarka zata zama abar yasarwa, saboda fushin da kake yi da iyayenka.
Ina rokon Allah ya ji kan mahaifana da suka rasu tare da dukkan Al'ummar Musulmi da suka rigamu gidan gaskiya, albarkacin Manzon tsira da alayen sa (S.)
Abdullahi Alkarazubiy Tsafe
11022020