Abin lura| Zama azzalumi ba yana nufin sai masu karfin iko kan jama'a bane!!!



@Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bin Haroun Sigau.

Kai kanka talaka, fakiri zaka iya zama azzalumi, kuma kuyi tarayya a zalunci da manyan azzalumai. Wai iyazu billah.

Ganin ana zalunci kayi shiru, da nuna ko in kula shima zalunci ne, dole matsayinka na musulmi in kaga ana zalunci kayi maquarar abinda zaka iya don fita hakkin wanda ake zalunta, da kuma sauke uzuri wajen Allah.

Zaluntar Malam Zakzaky da almajiran sa ,hakika a wannan nahiya ba'a taba zalunci irin sa ba. Domin in ka lura zaluncin da ake ya hada dukkan nau'o'in zalunci. Su kuma a bangare ɗaya wadanda basu tare dashi suke ganin ma hanyar sa bata ce ke goya wa masu zaluncin baya.

Kaga kenen da masu goyon baya da masu zalunci duk sunan su azzalumai. Kuma tabbas, Allah saiya tuhume su akan zaluncin da suke yi. Munsan jarrabawa ce da Allah ke jarabtar manyan bayin sa, wannan yasa duk lokacin da Allah ya jartabe mu muke ƙara gode masa bisa jarrabawar sa da rokon ya bamu ikon cinye wa...

Allah tabbatar da duga-dugan mu kan wannan hanya ta iyalan Manzon Allah (S). Ya bamu ikon jure duk wata jarabawa tasa.

#FreeZakzaky
#FreeUmmaZeenah

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post