Zunubin Wanda Yayi Kisan Kai Bisa Zalunci!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @

KADA KA YARDA KA KASHE WANI TUN FARANTAWA WANI RAI

Abu alkhairi ko rabon lahira ga wanda ya kashe ran wani bisa zalunci, ko don ya farantawa wani azzalumi rai.

Duk wanda ya kuskura ya kashe rai ta mutum don nemawa wani azzalumi daukakar duniya , to, ya sani cewa laifin wannan kisa na kansa. Idan kuma sa shi akayi , to, za suyi tarayya cikin zunubin kisan rai da gangan.

Ya zo cikin wani hadisi daga Abdullahi Bn  Mas'uda , daga Annabi (S.A.W.W)cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’  Wani mutum zai zo (ranar alqiyama )riqe da hannun wani mutum , sai yace, ‘’ Yaa  Ubangiji !Wannan ne ya kashe ni .‘’ Sai  Allah yace masa ;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ DON MENENE KA KASHE SHI ?‘’

Sai yace; ‘’ Na kashe shi ne don daukaka ta kasance gare ka .‘’ Sai Yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ TO, LALLE (daukaka )TANA GARE NI.‘’

‘’ Sa'annan wani mutum ya zo riqe da hannun wani mutum yace, ‘’ Wannan ne ya kashe ni .‘’ Sai  Allah (T )yace masa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ DON MENENE KA KASHE SHI?‘’ Sai yace,

‘’ Na kashe shi ne don daukaka ta kasance ga wane-da-wane .‘’  Sai Allah (S.W.A  )yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE KUWA ITA (daukakar )BA ZA TA KASANCE GA WANEN BA !‘’  Sai (wanda yayi kisan )ya koma da zunubinsa.‘’

(Nisa'i ne ya riwaito hadisin )

            DARASI
        ――――――

Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, duk wata rai da za ka kashe ko da kuwa ta kafiri ce ba bisa haqqi ba, to, zunubin wannan mummunan aiki na kanka da kuma kan wanda ya sa ka aikatawa. Ba za ka taba samun daukaka ko samarwa wani daukaka ta hanyar kashe rai bisa zalunci ba.

Inda ake samun daukaka kawai shine ta hanyar yaqar maqiya Allah don samarwa addinin muslimci 'yanci, ka kashe ko a kashe ka.

Saboda haka ku sani yaa ku Karnukan azzalumai da kafirai, mummuman aikinku da kuka aikata na nan jiranku ranar sakamako.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      08126385470

~16th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post