Zaluncin da ake a najeriya yafi karfin na falasdinawa domin an riga an sayar da kasar ne ga yahudawa




Sheihk yakubu yahaya katsina



–Sheikh Yaqoub Yahaya Katsina.

“Wannan fitowa da muke, karba kiran Manzon Allah  (s.a.w.w) ne, Manzon Allah (s.a.w w) yana cewa, wanda ya ji wani Musulmi koda daga karshen Duniya ne yana neman taimako ya kasance dayan Musulmin bai agaza masa da abin da yake iyawa ba, to shi ba Musulmin kwarai bane, wannan shi ne abin da muke iyawa, alal aqalla mun qarawa Yahudawa bakin ciki akan cewa wannan dandazon namu a ko'ina da muke irin wannan sawa'un a Abuja ne ko a Kaduna ne ko a Kano ne ko a Katsina ne ko a Sakkwato ne ko a Yola ne ko a Jos ne ko a Poteskum ne, kai koma a inane a kasarnan to duk cikar mu makiya Yahudawa ne.”

“Kuma gudun muwar abin da muke iya yi kenan a yanzu akansu, idan muka sami damar da ta wuce wannan zamu yi. Fiye da wannan fitowar da muke yi 
Muzahara domin taimakon raunanan Musulmin Falastinu idan muka samu za mu yi, idan muka sami damar da zamu taka muje har a can kasar ta Falastinu to zamu je, idan  wakilai muke da damar da zamu aika, zamu aika ne, sai su wakilcemu su yi abin da ya kamata.”

“Haka kuma wannan fitowar da muke a duk jum'ar karshen watan Ramadana a bisa irshadin Imam Khumaini (q.s) mun sani a bisa kaddarawa koda yau ace Sayyid Ali Khamna'i zai fito yace a bana duk duniya ba za a yi Muzaharar Qudus ba to muna sanya rai akan zai ce ban da Najeriya, mu a Najeriya mu yi, saboda irin tsabar zaluncin da yake gudana a Najeriya wanda kusanma qila za mu iya cewa ya zarce na Falastinawa, ta inda ya kasance mu anan Najeriya ba wai kawai su Yahudawan sun zo sun kwaci kasar bane, a a shugabannin kasar tamu ce suka dauki kasar suka mika musu.”

Wannan Wani Yanki Ne Na Jawabin Da Wakilin 'Yan Uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky(h) Na garin Katsina Sheikh Yaqoub Yahaya Katsina Ya Gabatar A Gurin Rufe Muzaharar Qudus Ta SHEKARAR Data Gabata A Garin Katsina.

Ma'asuma Nigerian news update tare da mudassir bara'a malumfashi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post