
Daga zaben shugaba makaranta Rigima ya barke a Jami'ar ABU Zariya.
Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Obi na Onitsha, Igwe Alfred Achebe, ya sa baki a kan rikicin da yake neman barkewa a Jami’ar a dalilin zaben sabon mataimakin shugaban Jami’ar. Shugaban ya bukaci Ma’aikatar Ilimi ta kasa da hukumar kula da Jami’o’in ta kasa (NUC), da su hanzarta daukan matakan ganin an warware matsalar.
Wakilinmu ya nakalto cewa, Basaraken ya aike da bukatar hakan ne a cikin wata wasika da ya aike wa babban Sakataren hukumar ta NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, inda ya ce rikicin zai iya haifar da rashin zaman lafiya a cikin Jami’ar. Obi Achebe, ya ce kasantuwar lokacin tattaunawa da dukkanin wadanda ake sa ran zama mataimakan shugaban Jami’ar na ranar 21 da 22 ga watan Janairu ya karato da kuma zaman da hukumar gudanarwa ta Jami’ar za ta yi domin fitar da sakankon karshe, yana da matukar mahimmanci a yi wani abu a kan lamarin cikin hanzari.
In har mai girma Minista bai gamsu da cewa hukumar gudanarwa ta Jami’ar za ta iya aiwatar da wannan mahimmin aiki da ke kanta ba, to yana da mahimmanci ya hanzarta kafa wani kwamiti mai zaman kansa a karkashin hukumar ta NUC wanda zai kammala aikin zaben sabon mataimakin shugaban Jami’ar, in ji Shugaban.
Sai dai kuma hukumar gudanarwar Jami’ar ta dakatar da batun zaben sabon mataimakin shugaban a sakamakon abin da ta kira da rikicin da ke ruruwa da kuma matsalar tsaro a cikin Jami’ar wanda ya samo asali daga zargin kauce wa hanyar da ya kamata a bi.” Wata wasika zuwa ga magatakardan Jami’ar, Malam Abdullahi Ahmed Kundila, wacce mataimakin shugaban Jami’ar mai ci a halin yanzun, Farfesa Ibrahim Garba, ya aike masa, ya umurce shi da ya dakatar da tattaunawa da dukkanin ‘yan takaran
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.