Za A Yi Wa ‘Yan Mata 10,000 Allurar Rigakafin Cutar Dajin Dake Kama Mahaifar Mace A Najeriya.

Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.

Kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Rotary international District 9110’ ta bayyana cewa za ta yi wa ‘yan mata 10,000 allurar rigakafin cutar dajin dake kama mahaifa a Najeriya. Kungiyar ta ce za ta hada hannu da wasu gwamnatocin jihohin kasar nan domin yi wa mata masu shekara 9 zuwa 13 allurar rigakafin cutar.

Shugaban kungiyar Jide Akeredolu ya ce rigakafin zai samar wa mace kariya daga kamuwa da cutar har iya tsawon rayuwar ta. Ya ce kungiyar zata yi haka ne domin samar wa mata kariya daga kamuwa daga cutar. Yin allurar rigakafin wannan cuta na da mahimmancin gaske ganin cewa wasu cututtuka da ake jingina su da cutar daji basu da magani har yanzu.

Idan ba a manta ba sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar a shekarar da ta gabata ya nuna cewa akalla mata 311,000 ne ke rasa rayukan su a duniya a dalilin kamuwa da cutar dajin dake kama al’aurar mace.
Bayanai sun nuna cewa mace kan kamu da cutar dajin dake kama al’aurar ta ne a dalilin saduwa da maza daban daban, kamuwa da cutar kanjamau, kamuwa da cutar sani da sauran su. Sannan mata masu shekaru 19 zuwa 49 suka fadawa cikin hadarin kamuwa da wannan cuta.


Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Update. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post