Yanzu-Yanzu: 'Yan Shi'a Suka yi Taron Manema Labarai A Abuja.

Almajiran Sheikh Zakzaky (H) sun gudanar da Taron Manema Labarai yau a Garin Abuja, kan yunkuri na kisan Sheikh Zakzaky da gwamantin Nigeriya take son aiwatarwa. Daga Wakilin Shafin Mu -Idishia Jos Harka musulunci a Nigeria karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) ta gudanar da taron Manema Labarai yau Laraba a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja. Anyi Taron Manema Labaran ne kan mummunan shirin Gwamnatin Dan Ta'addah Buhari na shirin Kashe Shaikh Zakzaky tare da kuma neman a saki Shaikh Zakzaky a Abuja. Manyan yan Jaridu da dama ne suka halarta na cikin kasa dama ketare, anyi taron lafiya an kuma ta shi lafiya, Allah ya kawar da mummunan shirin azzumar gwamnatin Nigeria akan Sheikh Zakzaky (H), ya kuma kubutar dashi daga hannusu. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. #FreeZakzky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post