Hargitsi ya kara rincabewa a kasar Afirka ta Kudu bayan ‘yan yankunan Keimoes da Upington na Arewacin Kasar Afirka ta Kudun, a safiyar Alhamis, sun ba ‘yan Nijeriya da ‘yan sauran kasashen duniya sa’o’i 12 da su tattara su bar yankunan. Adetola Olubajo, shugaban kungiyar ‘yan Nijeriya dake kasar Afirka ta Kudu, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.
Olubajo ya ce wannan ci gaban ya biyo bayan mummunan lamarin da ya auku ne tsakanin wani jami’in dan sanda da wani dan Nijeriya a ranar Laraba. Ya ce, an zargi wani dan Nijeriyan, kuma dan asalin Jihar Ebonyi da sukar dan sanda da makami mai suna Nico Bisagie, a yayin da wata hatsaniya ta hada su.
Olubajo ya ce, har yanzu dai ba a samu gamsasshen bayani ba a kan abin da ya hada su daga majiya kwakkwara balle a tantance dalilin sukar dan sandan. A halin yanzu kuma yana asibiti kwance a cikin mummunan hali. “Bayan aukuwar lamarin mai ba da tsoro, mazauna yankunan Keimoes da kewaye sun fito zanga-zanga tare da kone-konen kadarorin ‘yan wasu kasashen, musamman dai ‘yan Nijeriya, ” cewarsa.
Wannan harin ya yi kamari inda ya kai ga har an fatattaki ‘yan Nijeriya da wasu kasashen daga Upington. Daukin gaggawa da ‘yan sanda suka kawo a safiyar yau ne ya kwantar da tarzomar, amma ba duka ba. Wasu kafafen yada labaran cikin gida sun bayyana cewa, an cafke wasu bata-gari da suka dinga barnatar da dukiyoyin mutane,” Ya kara da bayyana cewa, wanda ake zargi da sukar dan sadan na hannun hukuma, kuma za a gurfanar dashi gaban kotu a ranar Litinin mai zuwa ko kafin nan
Daga Shafin Nigerian News Updates.
Tags:
Labaran Duniya