YAN BINDIGA SUN BAIYANA AGARIN MALUMFASHI TA JIHAR KATSINA

Yan bindiga sun bude wuta agarin Malumfashi, sun bindige Malamin SBRS har lahira 


Mlm umar isa futua Wanda Yan bindiga suka kashe agarin Malumfashi




 Da alama dai har yanzu tsuguni bai kare ba, sakamakon wani rahoto daya tabbatar da wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da sabon farmaki a karamar hukumar Malumfashi ta jahar Katsina. Jaridar Katsina Post ta ruwaito miyagun sun kai samamen ne da yammyacin Litinin, 6 ga watan Janairu ga wasu al’ummomin karamar hukumar Malumfashi, wanda hakan yasa jama’a da dama tserewa daga muhallansu domin tsira da ransu. 
 Sai dai a sakamakon harin wani malamin jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, wanda ke koyarwa a cibiyar horas da daliban da suka kammala karatun sakandari kafin su shiga jami’a, SBRS, ya gamu da ajalinsa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta tabbatar. Amma rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina ta tura jami’an zuwa inda lamarin ya auku domin fuskantar yan bindigan, inda suka dinga musayar wuta a tsakaninsu. A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Katsina ta tabbatar da satar mutane 7 da wasu gungun miyagu masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba dasu yayin da suka tare manyan motocin Pijo J5 a daren Lahadin da ta gabata. Motocin suna kan hanyarsy ta komawa garin Batsari ne daga wani kasuwan mako mako dake ciki a karamar hukumar Jibia a lokacin da suka ci karo da miyagun a daidai kauyen Ruma. Majiyoyi sun bayyana cewar bayan yan bindigan sun tare motocin, sai suka kwashe fasinjojin motar gaba daya da yawansu ya kai 38 zuwa 40 suka tasa keyarsu zuwa cikin daji. Amma rundunar Yansandan ta musanta wannan rahoto, inda tace mutane 7 kadai yan bindigan suka yi garkuwa dasu. Rundunar ta bayyana sunayen mutanen kamar haka; Mu’azu Yasore, Alhaji Nuhu, Kabiru Hashimu, Dan Asibi Tela, Sani Kokari, Nura Shambal da kuma Ali Dan Maituwo.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post