
Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.
Lura da yadda ’yan mata masu karancin shekaru suke fantsama cikin manyan birane a kasar nan don yi karuwanci inda wadansu ke karuwancin kai-tsaye, wadansu kuma su fake da wasu sana’o’i, kamar dirama ko rawar solo yayin da wadansu ma suke karuwancin a gaban iyayensu. Wata kafar yada labarai ta gudanar da bincike na musamman a kan meke haddasa wannan al’amari? Wace riba ko akasi suke samu? Kuma wadanne hadurra suke gamuwa da su a yayin wannan rayuwa tasu? Wakilan wannan kafa ta sada zumunta sun binciko yadda abubuwa suke a wasu daga cikin manyan biranenmu kamar haka:
A Jihar Kaduna, wakilinmu ya gano cewa sana’ar karuwanci tana neman zama ruwan-dare a tsakanin ’yan mata masu kananan shekaru a wasu unguwanni da ke a tsakiyar garin Kaduna. Yawancin ’yan matan da suka tsinci kansu a cikin karuwanci shekarunsu ba su wuce 16 zuwa 20 ba. Kuma akasarinsu suna zaune ne a gidajen iyayensu, kodayake akwai wadanda suka fito daga wasu jihohi suka zo Kaduna domin yawon duniya.
Yawancin ’yan matan suna alakanta dalilinsu na shiga bariki ne da rashin kulawa daga iyayensu, wadansu kuma sukan ce akwai son kai da kuma auren dole da ake yi musu. Binciken da ya gudanar ta fahimci cewa wadansu daga cikin ’yan matan da suke sana’ar karuwancin sun fito ne daga unguwannin Rigasa da Tudun Wada da Kawo da Nasarawa da Badarawa da sauransu. Akwai kuma wadanda suka fito daga jihohin Jigawa da Neja da sauransu.
Wadansu sun baro gidajen iyayensu ne suka shigo jihar, inda suka kama dakuna a otel-otel suna holewarsu. Wakilinmu ya gano cewa ’yan matan suna haduwa da mazan ne a gidajen dirama ko na dambe da ke garin, inda wadansu kuma kiransu ake yi a waya su hada su da mazan.
Akwai kuma wadansu da kawalai matasa maza da suke hada su da maza, inda su kuma kawalan ake ba su la’ada. Binciken ya nuna cewa mafiya yawan ’yan matan ana biyansu ne daga Naira dubu uku zuwa Naira dubu goma. ’Yan matan suna kuma kama dakuna ne a otel a wasu unguwanni, inda suke haduwa da mazan su yi lalata.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.