Yadda Ake Karanta Ziyarar Sayyada Ma'asumah Fatima (S.A)!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Yana daga cikin ibadodi ziyarar bayin Allah salihai ga duk mumini, musamman karanta ziyarar Manzon Allah (S.A .W.W )da ta iyalansa (A.S ).

Ita wannan ziyara ana iya yinta da gangar jiki ga wanda ya sami iko, ga wanda bai sami iko ba kuma yakan iya karanta ziyarar daga duk inda yake.

Ya zo cikin wani hadisi daga Imam Sadiq (A.S )yana cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ DUK WANDA YA SAMI IKO TO, YA ZIYARCE MU.‘’

Sai aka tambaye shi cewa, ta yaya za a ziyarce su ga wanda ba tare da su (a raye )?

Sai yace,

‘’ DUK WANDA BAI SAMI IKON ZIYARTARMU (ta zahiri ba ), TO, YA ZIYARCI SALIHAN MASOYANMU, ZA A RUBUTA MUSU LADAR WADANDA SUKA ZIYARCE MU.‘’

Sannan kuma akwai ziyarori ma'asurai da ake karantawa ta ziyarar iyalan gidan Ma'aiki (A.S ). Ga kuma yadda ake karanta ta Sayyidah Ma'asumah (S.A ).

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE KI YAA KE MA'ASUMAH WACCE AKA ZALUNTA.

AMINCI A GARE KI YAA KE MAI TSARKI ABIN TSARKAKEWA.

AMINCI A GARE KI YAA KE WACCE AKA QWACEWA HAQQI.

YAA ALLAH KAYI SALATI BISA ANNABI MUHAMMAD DA IYALAN GIDANSA . KAYI SALATI A BISA BATULA MAI TSARKI, MAI GASKIYA, KATANGAGGIYA MAI TSORON ALLAH , WANKAKKIYA DAGA DATTI, YARDAJJIYA ABIN YARDARWA , TSARKAKEKKIYA , SHIRYAYYA WACCE AKA ZALUNTA DA QARFI, WACCE AKA QWACEWA HAQQI, WACCE AKA CUTAR DA MIJINTA , AKA KUMA KASHE 'YA'YANTA , FATIMAH 'YAR MANZON ALLAH (S.A.W.W ).‘’

Duk wanda ya karanta wannan ziyara gare ta bisa da ikhlasi, to, tamkar ya ziyarci qabarinta ne (S.A ).

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da  Ado  Isah  Guda.

08137925034-08126385470

~13th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post