Tuna Baya:/ Misalin tsarin mulkin zalincin nigeria kamar misalin gidan giya ne


      -SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H)!!!

“Abin da mutane za su lura shine, yau an wayi gari abin da yake tafiyar da kasar nan ba addinin Musulunci bane, kuma abin takaici shine, Musulmin ne ke tafiyar da shi. To, ba muna batun wa ke tafiyar da abin ba, muna batun mene ne ake tafiyarwa? Ba wane ne ke shugabanci ba, a kan me yake shugabanci? Abin da muke magana kenan. A kan me ake shugabanci? A kan Allah yace, Annabi ya ce? A’a! To, in ya so ya zama Alhaji wane (ke tafiyar da abin), in dai ba batun Allah yace, Manzonsa yace bane, to ba addini bane. Kasantuwarsa Alhaji wane bai mai da wannan abin addini ba.

“Bari na baku misali, yanzu don an samar da gidan giya (irin wacce ake saka ta a kwalba din nan), amma sai aka saka Alhaji Ibrahim ya zama shi ne Manajan gidan giyar, sai giyar ta zama halal? Sai aka ganka kana shan giyar, sai kace to ai ta Alhaji Ibrahim ce? Giyar Musulmi ce? Ka iya sha tunda yake giyan Musulmi ce (Musulmi ne manajan gidan giyan) sai ta zama halas? To , in dai ka Musuluntar da giya domin Alhaji Ibrahim ne ya dafa ta, to ka mai da (tsarin) Nijeriya Musulmi domin Musulmi ke shugabancinta. Alhali abin da yake shugabanci a kai ba abin da ya dace da Musulunci bane, sabanin ma Musuluncin ne.

“Yana da kyau mu gane cewa, idan abu ba Musulunci bane, bashi da wata maraba ko wane ne ma yake tafiyar da wannan abin. Akwai bambanci ne idan Mista John ne ko Alhaji Ibrahim ne yake tafiyar da gidan giya? Ko ya zama John ko ya zama Alhaji Ibrahim duk daya, in dai giya ce giya ce, haramun ne a sha ta. Allah ya tsinewa mai shan ta da mai dafa ta da mai sayar da ita, da mai raba ta da mai daukanta da abin ma da ake dakonta da shi. Saboda haka idan Alhaji Ibrahim ne manajan gidan giya, to tsinanne ne shi. Idan John ne, tsinanne ne. Tsinewa ba za ta hau kan John ta sauka a kan Alhaji Ibrahim ba, matukar dai giyan ce.

“Saboda haka babu wani maraba, kasantuwar Musulmi ke rike da al’amari bai mai da al’amarin Musulunci ba, sai randa aka ce doka ta Allah (T) ne za a bi. Kuma ya zama hankoronmu a bi dokar Allah, ba wai ace Musulmi ne ke tafiyar da abin da ya sabawa na Allah ba.

“Kuma bamu bukatar Musulmi ya tafi da abin da ya sabawa na Allah a matakin farko na bin abin da Allah yace a yi. Mu sabi Allah a matakin farko domin mu zo mu bi Allah. Wannan saboda Allah muna bukatar haka nan? Kafin ka bi Allah kana bukatar sai ka saba mishi domin ka bi shi? Me zai sa ba za ka bi shi kai tsaye ba tare da ka bi ta hanyar saba mishi ba?

“Ba mu da bukatar mu rike hanyar kafirci a matsayin matakin farko kafin mu tsai da Musulunci, abin da muke cewa kenan. Kuma ba ma wani Manzon da Allah (T) ya taba aikowa domin ya gusar da barna wanda al’ummarsa take a kai, ya zama ya aikata wannan barnar a matsayin matakin farko kafin ya gusar da ita barnar.”

- Bangaren Jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky a garin Rimi, a shekarar 1990. Kimanin shekaru 28 da suka gabata. Kuma Alhamdulillah, har yanzu Shaikh Zakzaky a kan wannan yake bai sauya ba. A kan hakan ne kuma mahukuntan Nijeriya ke yakarsa ba dare ba rana da nufin kawar da shi da da’awarsa.

Auwal Yusuf Muhammad
Ma'asumah Najeria news Updet
#18/1/2020
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post