Trump Ya Gargadi Ayatollah Khamne'i Kan Yiwa Turai Barazana

Ko maganar Donald Trump zai yi tasiri ga Janhuriyar musulunci ta Iran ! Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos. Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi jagoran juyin-juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei kan kalamansa na jiya juma’a da ke zargin Washington da rura wuta kan kuskuren harbor jirgin Ukraine da Iran ta yi dama batun nukiliyar kasar baya ga sabbin takunkuman da Trump ya sake laftawa Tehran. Cikin sakon Twitter da Trump ya wallafa ya gargadi Khamnei da ya kula da kalamansa, kan barazanar da ya ke kokarin yiwa Amurkan da nahiyar Turai dungurugum, yana mai cewa babban kuskurene yadda Khamene'i ya bayyana kasashen Faransa, Birtaniya da kuma Jamus a matsayin ‘yan amshin shata ga Amurkan. Cikin kalaman na Trump ya ce maimakon Khamnei ya tsaya tsara kalamai don muzanta kasashen kamata ya yi, yayi tunanin halin da tattalin arzikin kasarsa ke ciki da kuma rigingimun da ke gabanta baya ga halin matsin rayuwar da al’ummarsa ke ciki. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post