Kungiyar yan’uwa Musulmai almajiran sayyid ibrahim YaQub al-zakzaky (h) da akafi Sani da Yan Shi’a a Najeriya a ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, ta jagoranci wani tattaki hanyar Banex, yankin Wuse har zuwa shataletalen Burger a babbar birnin tarayya, Abuja.
Mambobin na IMN na zanga-zanga ne akan kisan babban kwamandan sojin Iran, Qasem Soleimani biyo bayan wani hari da kasar Amurka ta kai Kansa a ranar Juma’a da ya gabata.
Mambobin kungiyar na kuma neman a saki shugabansu El-Zakzaky da matarsa, Zeenat wadanda ke tsare a hannun hukumar DSS a jihar Kaduna.
Fusatattun masu zanga-zangan sun fito unguwannin Abuja, suna wakokin sukar gwamnatin Amurka.
Sun kuma kona tutar Amurka sannan sun kasance dauke da allunan sukar kisan babban janar din Iran.
A baya mun ji cewa babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu ya umarci jami’an Yansandan Najeriya su zauna a cikin shiri ta yadda komai ta fanjama fanjam.
Tags:
Labaran Duniya