Tarihin rayuwar sheikh Dr. Abduljabbar nasiru kwbara







Sarkin Gida, Sarkin Kogo, Amirul-wa’izina, da Sahibut-tahalil, na daga sunaye ko lakaban da mabiyansa ke kiransa da shi.
An haifi Malam Abduljabbar 2/7/1970 a unguwar Kabara dake Kano. Mahaifinsa sanannen malamin addinin Musulunci ne, wato Shaikh Nasir Kabara. An haife shi a lokacin mahaifinsa ya tafi Bagdad (Iraq) don ziyartar Sidi Abdulkadir. Lokacin da ya dawo sai ya sa masa Abduljabbar, irin sunan dan Sidi Abdulkadir, ya ba da labarin cewa akwai wani hali da yake tsakaninsa da Allah, amma sai ya dade wannan yanayin baya zuwar masa, ya dinga rokon Allah ya dawo masa da yanayin, amma bai dawo masa da shi ba sai a wannan ziyarar da ya tsaya a kabarin Abduljabbar din sai Allah ya dawo masa da yanayin. Kuma da yake kabarin Shaikh Abduljabbar din a farkon hubbaren Sidi Abdulkadir din yake, yakan kira shi da Sarkin Gida. Yana dawowa ya tarar matarsa Sayyyida Zinatud-dini ta haifi namiji, sai ya sa masa Abduljabbar, yake masa lakabi da Sarkin Gida ko Jabbariy.
Tasowar malamin a gidan ilimi da hidimta wa addini ce ta cusa masa son ilimi, yadda ya kifu a gaban babban malaminsa kuma mahaifinsa, ya dinga kwankwadar fannonin ilimai, tare da taimakon kaifin basira da zurfin hadda da Allah ya ba shi. Amma duk da haka ya zabi ya tafi neman ilimi wajen jahar Kano, don samun wadataccen lokaci. Kai tsaye Sokoto ya nufa ya sauka a gidan Shehu Muhammadu Bello dan Abubakar Kanwa.
Kamar yadda yake ba da labari, a farkon al’amarinsa baya saurin rike karatu, har sai watarana da wani bakon makaho ya ziyarci mahaifinsa, ‘ya’yan gidan suka dinga zuwa gaisar da shi daya-bayan-daya. Duk wanda ya gaisar da shi sai ya dora hannunsa a kan kirjinsa sannan ya bayyana irin matsalolin da yake fuskanta da hasken da Allah ya haska masa na firasa. Lokacin da malamin ya ziyarce shi sai ya ce matsalarsa ba ya saurin rike karatu, sai mahaifinsa ya nemi ya yi masa addu’a, kuma yi yi masa “Tun daga lokacin na zamo daga wadanda suka fi iya hadda a sa’annina, daga ranar zai yi wahala na haddace wani abu na ilimi na manta da shi” (Kamar yadda ya fada : Littafinsa Mukaddimatul-azifa juz’i na daya, wanda daga shi muka fassaro jigon tarihin nan).
Ya yi karatun Alkur’ani a hannun Malam Abbas (Mu’addibus-sibyan), da kuma a makarantar Malam Ibrahim mai garaje, da makarantar Mahiru Sharif Bala (Har ya sauke).
Litattafan ilimi kuwa yawanci a gaban mahaifinsa ya saukesu, domin bacci ne kawai yake hana shi daukar karatu a wurinsa. Ya kuma yi karatu a wurin malamai irinsu Shaikh Malam Dan Yalwa.
A bangaren karatun zamani kuwa, ya yi Primary a makarantar Ma’ahaduddin ta mahaifinsa. Sai Junior secondary a G.A.T.C Gwale (Wadda yanzu ta koma G.A.C)a shekarar 1989, ya yi Senior a Aliya. Inda ya tafi Iraki don karatun jami’a a fannin addinin Musulunci (Islamic Studies) don samun shaidar digiri.
Malamin mabiyin mazhabar Malikiyya ne. A akida kuma Ash’ariyya. A darika kuma Kadiriyya, wanda shi shehi ne ma na wani bangare a cikinta, wato Kadiriyya Riyadul-janna. Duk da yana tasirantar da abinda ya tabbata a gare shi a matsayin hujja da dalili. Dalili na iya hada shi da kowa kuma yana iya raba shi da kowa. Yana da tsananin riko da abinda ya gamsu da hujjarsa. A matafiyarsa, zai iya gamsuwa da kowane ra’ayi in dalili ya tabbatar masa, zai kuma iya barin duk wata akida in dalili ya kawar masa da ita, shi ya sa yake maimaita Nahnu Atba’ud-dalil ainama mala namilu. Kuma an fi sanin mabiyansa da ‘yan kogo (Wato As habul kahfi), ko kuma ‘Yan Kowaye, saboda tarbiyyarsu ta cewa kowaye Annabi ya fi shi.
Nibrasud-da’awa shi ne sunan wata wakar Larabci da ya rubuta wa mabiyansa a matsayin kundin tsarin tafiyar da da’awarsu.
Riyadul janna shi ne sunan da ya kira kundin zikiran Annabi da ya lazimtawa mabiyansa biya shi, tare da fifita shi kan kowane zikiri na shehunansu.
Yakan fifita karantar da litattafan da ya rubuta da hannunsa a majalisansa na Lahadi a Sabuwar Gandu, da na Juma’a a As’habul-kahfi.
Daga ayyukansa akwai:-
Kafa cibiyar As’habul kahfi war-Rakim, wadda ta haura shekaru ashirin da kafawa. Wadda ke da mabiya a jahohin Nijeriya da wajenta, kuma cibiyarta ke Sani Mai nage cikin babban masallacinsa na Jami’u Amiril-Jaishi.
Zawiyyar Shehu Abdullahi Sika, mai dauke da masallaci da laburaren Darul Kur’an.
Darul hijira makarantar ilimi a Mariri dake karamar hukumar Tarauni.
Samar da tarin masallatai a sassan Nijeriya da wajenta karkashin mabiyansa.
Makarantu a lugu da sakon da yake da mabiya.
Darul-Kadiriyya Riyadhul-Janna Cibiyar darikar da yake jagoranta, a unguwar Sabuwar Gandu Kano.
Katafaren dakin karatu Albahrul- Adlas da yake ginawa a Sani mainage.
Yada ilimi a majalisai da kafofin sadarwa, da kuma a tarurruka na gida da na kasa da kasa, inda ya ziyarci kasashe masu dimbin yawa.
Rubuta litattafai masu yawa, musamman a fagen raddi ko kariya ko kafa akidar da yake kai. Daga cikinsu akwai :-
Mukaddimatul-Azifa
Al-Ababil
Asa Musa
Arrauhu war Raihan Fis salati wat taslim ala Sayyidi waladi Adnan
Alhayatu Ba’adal maut
Jauful

mudansirbaraamalumfashi@gmail.com 08163392448

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post