Duk da karin matsin lamba da gwamnatin
Buhari ke fuskanta daga ciki da wajen kasar
nan saboda matsayar da Kotun Hukunta
Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ke birnin
Hague ta dauka na gudanar da bincike
dangane da cin zarafin Bil’adama wanda
wannan gwamnati ta aikata a yayin harin
‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a
Nijeriya a cikin watan Disambar 2015, sai aka
samu karin kokarin wawitar da batun kuma da
bayyana cewa sassaukan lamari ne. Wannan
lamari ya kai kololuwa a cikin ‘yan kwanakin da
suka gabata a lokacin da Gwamnan Jihar
Kaduna, Nasiru El-rufa’i ya yi ta kokarin cakuda
gaskiya da karya, abin da kuma aka san shi da
shi.
Bisa wannan matsaya ta makirci, ya lashi
takobin cewa matukar yana a matsayin
Gwamnan Jihar Kaduna, Shaikh Ibraheem
Zakzaky zai kasance a tsare. Kamar yadda
Gwamnan ya ce, Shaikh Zakzaky yana
fuskantar shari’a ne kan laifukan da ya kwashe
shekaru talatin yana aikatawa
da shi da mabiyansa a cikin garin Zariya.
Amma sabanin haka nan, bayan yi wa gidan
Shaikh Zakzaky kawanya a cikin watan
Disamban 2015 da kuma abin da ya biyo baya
na kashe daruruwan mabiyansa, ciki har da
‘ya’yansa da ‘yan’uwansa da jami’an tsaro
Sojojin Nijeriya suka aikata, Shaikh Zakzaky da
mai dakinsa, Malama Zeenah an harbe su da
bindiga, aka kama su aka tsare. Shaikh
Zakzaky da mabiyansa sune kasa ta zalunta,
aka kuma yi wa laifuka na ta’addanci, amma
ba su suka aikata laifi ba. Hukumar tsaro ta
farin kaya (DSS) ta tsare su ba bisa ka’ida ba,
kuma ba tare da tuhumar su da aikata wani
laifi ba har sai zuwa cikin watan Mayu 2018, a
yayin da matsin lamba kan gwamnati ta sake
su ya yi mata tsanani. A wancan lokacin ne
gwamnati ta yi
tunani tare da kirkirar tuhumar su da kagaggun
laifuka na tunzura mabiyansa da aikata laifuka.
Kafin nan kuwa, gwamnati ta yi ta kame-
kamen bayyana dalilan da ya sanya take ci
gaba da tsare su. Gwamnati ta bayyana karara
cewa, ana tsare ne da Shaikh Zakzaky domin
ba shi ‘Kariya,’ ba saboda ya aikata wani laifi
ba. Haka nan kuma sun bayyana cewa, mai
dakinsa, Malama Zeenah ba ana tsare da ita
ba ne, ‘kawai tana zauna ne domin taya mai
gidanta zama,’ don haka tana da damar tafiya
a duk lokacin da take bukata. To, don haka
wadanne laifuka ne Gwamna El-rufa’i yake
cewa an aikata?
Haka zalika duk kafin wadannan ma, a ranar 2
ga watan Disambar 2016, babbar Kotu da ke
Abuja wacce mai girma mai Shari’a G.O
Kolawale (Wanda yanzu yake a babbar Kotun
daukaka kara) ya zartar da hukuncin cewa
kamawa da tsarewar da aka yi wa Shaikh
Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenah ba
abu ba ne wanda yake bisa doka kuma lamari
ne wanda ya saba wa Kundin tsarin Mulkin
Kasa (Constitution). Haka nan ita ma Hukumar
Bincike wadda gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa
ta tabbatar da cewa Sojojin tarayyar Nijeriya
sun kashe ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh
Zakzaky 347 a yayin da suka yi wa gidan
Shaikh Zakzaky kawanya tare kuma da rufe
gawawwakin wadanda suka kashe a cikin
Kabari na bai-daya a boye cikin tsakar dare,
tare kuma da zartar da cewa a kama manyan
jami’an tsaron da ke da hannu a cikin wannan
lamari a kuma gurfanar da su a gaban shari’a.
Tun daga wancan lokacin gwamnati take ta
nuku-nuku, tare kuma da nuna cewa ba shirye
suke ba da aikata wannan shawara ta
hukumar bincike ba dangane da wadannan
manyan jami’an sojoji. Abin mamaki, mamadin
a zartar da wannan shawara ta hukumar
bincike, sai ga shi an buge da kama daruruwan
‘yan’uwa Musulmi na Harkar Musulunci a
Nijeriya tare da gurfanar da su a gaban shari’a
ana tuhumar su da laifin kashe wani jami’in
Soja, wanda bisa hatsari ‘yan uwansa Sojoji
suka harba da bindiga a yayin harin nasu na
ta’addanci. Babbar kotun Jihar Kaduna ta
wanke wadannan ‘yan’uwa daga dukkanin
kagaggun laifuka da aka tuhume su da
aikatawa, ta sallame su tare kuma da nisanta
su daga aikata laifukan da aka tuhume su da
aikatawa. To, don haka, shin wai wadanne
laifuka ne kuma Gwamna El-rufa’i yake cewa
an aikata?
Ikirarin karya da Gwamna El-rufa’i ya yi cewa
Kotu ce kadai ke da hurumi da kuma ikon sakin
Shaikh Zakzaky ba shi da tushe bisa la’akari
da abin da yake a bayyane. Da farko,
kagaggun laifukan da aka tuhume shi da
aikatawa na tunzurawa da kuma taimakawa
wajen aikata kisan kai (domin salon makirci na
ci gaba da tsare shi) irin sa aka tuhumi wasu
‘yan’uwa, wanda babbar Kotun Jihar Kaduna
da kuma kotun daukaka kara ta yi watsi da su.
Abu na biyu kuma, babbar kotun Kasa da ke
Abuja ta zartar da hukuncin tsare shi da ake yi
a matsayin lamarin da ya sabawa doka, ya
kuma yi hannun riga da kundin tsarin Mulkin
Kasa, don haka ta bayar da umarnin sakin sa.
Umarnin da har yanzu gwamnati ta ki
aiwatarwa bisa rena kotu. Abu na uku kuwa, ko
a lokacin da babbar kotun Jihar Kaduna ta ba
wa Shaikh Zakzaky damar fita kasar waje
domin neman lafiyarsa, El-rufa’i bai saduda da
hukuncin ba. Ya dauki matakai na yin kafar
Ungulu
dangane da wannan bayar da beli domin tafiya
neman magani, ta hanyar sanya wadansu
tsauraran ka’idoji da sharudda wadanda Kotun
ba ta gindaya su ba. Tabbas, kuma karara,
Gwamna El-rufa’i, kamar Ubangidansa wanda
yake yi wa aiki, Janar Buhari, ba masu mutunta
doka da oda ba ne.
Daga karshe, za mu so sanar da Gwamna El-
rufa’i da Ubangidansa cewa ranar biyan bashin
ayyukan da suka aikata na nan zuwa nan
kusa. Adalci zai tabbata, kuma ba wani girman
kazafi ko ci da ceto ko yin amfani da karfin iko
ba ta hanyar da ta dace ba da zai hana
wannan guguwa ta adalci daga lakume su
dukkanin su. Ta janibinmu, za mu ci gaba da
fafutukarmu ta lumana ba tare da gajiyawa ba
har sai mun tabbatar da an yi adalci ga
wadanda kisan kiyashin Zariya na watan
Disamba 2015 ya rutsa da su, kuma Shaikh
Zakzaky da ma sauran wadanda ake ci gaba
da tsare su sun sami ’yancinsu.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA
HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
SKYPE: Ibrahim.musa42
12/01/2020
Tags:
Labaran Duniya