TAKAITACCEN TARIHIN JANAR QASIM SULAIMANIY.


Shahid Janar Qasim Sulaimaniy, an haife shi 11/03/1955. Ya shiga sojan sa kai, na dakarun kare juyin Musulunci a shekarar 1979. Bayan nan ya shiga fagen jahadi gadan-gadan, lokacin yakin da Saddam ya kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a lokacin yana dan shekara Ishirin da wani abu, mafi yawan aiyuka a yakin da shi a ciki. Ya samu raunuka masu tsanani a harin hanyar Qudus a lokacin yakin Saddam kan Iran.
.
bayan kammala yakin, a cikin tis'inoni, ya zama jagoran dakarun kare juyin musulinci na Iran, a yankin Kirman. A shekarar 1998, aka aiyana shi a maysayin kwamandan rundunar Quds, wadda runduna ce ta musamman, ta dakarun kare Juyin Musulunci. A shekarar 2011, Jagoran juyin Musulunci na Iran Ayatullah Khamenei ya daga darajarsa ta soja zuwa cikakken Janar.
.
Bayan ya ta'addan da Amurka ta horar, wato ISIL ko Daesh, sun mamaye wurare da dama a Iraqi sa Syria, Janar Sulaimaniy ya baiwa wadannan kasashe gudunmawa me yawa, wajen yakar wadannan yan ta'adda. Ya kasance yana kula kai tsaye da yakoki da dama da aka fafata da wadannan yan ta'adda, abinda ya taimaka wajen murkushe su a wadannan kasashen.
.
A kowane loakci, Janar Sulaimanie yana jaddada cewa taimakawa al'amarin Palastine da Palastinawa abu ne da zai cigaba, domin hakan na daga cikin shika shikan gwagwarmaya, da aqidun gwagwarmaya da shi ya yi imani da su. Kuma a wurinsa Palastine aqida ce.
.
Janar Sulaimanie ana masa lakabi da shahidi me rai, domin ya kutsa yakoki da dama masu wahala da tsanani ba tare da tsoro ba ko ta raddadi, kuma abunda yake buri a kulkum shi ne ya yi shahada a tafarkin Allah.
.
A cikin wani hari irin na matsorata da Amurka ta kaddamar a kusa filin jirgin saman Bagdad a jiya, wanda ta hari motar da ke dauke da janar Sulaimanie, sai burinsa ya cika, inda ya samu shahada alhali yana kan hanyar gaskiya.
.
Wannan ne kuma tafsirin fadin Allah madaukakin sarki:
" ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺭﺟﺎﻝ ﺻﺪﻗﻮﺍ ﻣﺎ ﻋﺎﻫﺪﻭﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻤﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻗﻀﻰ ﻧﺤﺒﻪ ﻭﻣﻨﻬﻢ ﻣﻦ ﻳﻨﺘﻈﺮ ﻭﻣﺎ ﺑﺪﻟﻮﺍ ﺗﺒﺪﻳﻼ ".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post