Ta'aziyyar Imam Ali Ga Manzon Allah (S.a.w.w)!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

IMAM ALI (A.S )NE YA BISNE SAYYIDAH FATIMAH (S.A )

Bayan ta'addancin da aka yiwa Sayyidah Fatimah (S.A )wanda yayi sanadin wafatinta ranar 12th Jimada-Ulah 11 (B.H ), kwana 75 daga wafatin ,mahaifinta (S.A.W.W ), tana da shekaru 18 kenan a duniya .

Sakamakon halin da ake ciki na qiyayya gare ta (S .A )yayi sanadin Imam Ali (A.S )ne ya bisne ta shi kadai cikin dare.

Gama yi mata sitira (jana'iza ) ke da,wuya sai ya fuskanci inda Manzon Allah (S.A.W.W )yake , yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ AMINCI A GARE KA YAA MANZON ALLAH. HAQURIN RABUWA DA KAI YA YI MIN KADAN, RABUWA DA FATIMAH  YA RAUNANA JIKINA, SAI DAI INA MAI KOYI DA SUNNONINKA .

HAQIQA QABARINKA YA RINJAYENI, ZUCIYARKA NA NAN TSAKANIN ZUCIYATA DA QIRJINA , TABBAS MAGANAR ALLAH TA TABBATAR DA FADINSA .

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ HAQIQA DAGA ALLAH MUKE KUMA GARE SHI MUKE KOMAWA.‘’

TO, HAQIQA NA KOMA GABA 'DAYA ZUWA GARE SHI , DOMIN NA YI RIQO DA KYAKKYAWAR HANYA, ITA KUMA FATIMAH TA SAMU DAMAR HADUWA DA KAI . BABU ABINDA YA KAI RABUWA SA KAI MUNI YAA MANZON ALLAH (S.A.W.W )! BAQIN CIKINA MAI WANZUWA NE, QUNCIN ZUCIYA KUMA BA ZAI FICE DAGA RAINA BA, TARE DA BAQIN CIKI MAI QUNCI !INA KAI KUKANA 😭😭😭😭😭😭😭😭 ZUWA GA ALLAH.

YAA MANZON ALLAH, FATIMAH ZA TA BA KA LABARIN YADDA AL'UMMARKA SUKA HANA TA HAQQOQINTA. YANAYIN  DA KA GANTA MA YA ISA ZAMA SHAIDA A GARE KA. GA KYAKKYAWAR TA'AZIYYATA ZUWA GARE KA YAA MA'AIKIN ALLAH . AMINCIN ALLAH DA YARDARSA SU TABBATA A GARE KA.‘’

Muma muna yi maka ta'aziyyah yaa Ma'aikin Allah !

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da Ado  Isah Guda.

       08126385470

~12th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post