MA’ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Godiya ga Allah subahanahu wata ala daya bamu damar gudanar da wannan shiri a karon mu na farko cikin sabon tsari da akayi dan guda danar da shirye shirye a wannan shafi mai girma da farantawa mabiyan sa wato shafin (Maasumah Nigerian News Update).
Kafin na fara abin da shi ya hadamu zanyi amfani da damar nan nayi abin da banyi ba a baya sakamakon wasu yan dalilai, zan fara da mika ta’aziyata ga “yan uwa “yan jarida musamman ma’aikatan shafin ma’asumah nigerian news update dama sauran “ yan uwa gaba da na rashin babban abokin aiki mutum nagari mai farantawa kowa abun alfahari kuma garemu, ina mai tayamu juyayin rashin sa.
Da farko da yake wannan shi ne darasi na farko to zai zama kamar gabatar wane zuwaga darusan mu na gaba dan haka muna saran zakuci gaba da kasan cewa damu dan daukar darusan da zamu kawo maku anan gaba, kar kaji nace gabatarwa zamuyi kaki karanta gabatarwa a’a akwai abubuwa da yawan gaske a cikinta.
Menene Fasaha:- Da yake nayi bincike kadan akanta to nidai ina kallon fasaha ne a wani abu na rayuwa kuma dole sai dashi ka rayu saboda kuwa a wani karatuna ya nunan hatta da cin abinci ko yin magana ko makamancin su ma fasahace, amma wasun mu basu gane hakan ba sun zata kawa waya da komfuta ne kawai fasaha wanda yasan su shi ne gwarzon fasaha a’a ai ko ba haka bane, saboda ita fasaha ta kasance wani ko wani bangare ne na rayuwa ta hanyar magana ne ko ta hanyar ko ta hanyar sarrafa abin da za’a ci ko ta hanyar meye to saika samu wannan yanayi na fasaha ya shigo ciki ba wai ta tsaya wa iya sahen amfani da na’urar sadarwa bane.
Dan haka kan ilimi irin na fasaha wannan shiri zaina zuwa muku kuma zamuna daukar abubuwan da kuka fi amfani dasu wajen amfani dasu a rayuwar ku muna yin bayani akai musamman waya da komfuta, kafar sadarwa dama sauran su.
Da akwai wani abu da yake damuna dan haka zan fara tashi dan sau dayawa sister zakaji ta kirani a waya ko text Ali shi’a ya zanyi rufe kaza dina mutane suna damuna.
Karki damu sister shin kin bude facebook kuma abokanki mazan suna daukar number ki suna kiranki ba tare da kin so ba? Zan yi magani matsalar yanzu.
Ko kuwa wani yan maki maganar da bata dace ba kinason gogeshi? Shima karki damu zaki koreshi gabadaya bazai sake ganin kiba.
Afuwan brothers shafin sayyada ne shiyasa na fada sister a karo na gaba kune a layi.
Ku ci gaba da kasan cewa damu duk ranar Laraba zamu koyar daku abu buwa da Allah ya sanar damu a bangaren fasahar zamani.
Tared
-Aliyu idris mohd shi’a
Tags:
Yanar gizo