Shifa Shahidi Ba Matacce Bane, Ko Da Kuwa Bakwa Ganin Sa!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Ba baqin cikin rabuwa da shahidi ake ba sai dai baqin cikin rasa gudumawar da ake samu daga gare shi. Sau da yawa ba a sanin haqiqanin fa'idantuwar da ake samu daga shahidanmu har sai bayan rabuwa da su hakan ke bayyana, domin anan ne ake gano cewa ashe akwai wasu gurabe da suka toshe wadanda samun masu toshe wadannan gurabe sai tsananin sa'a, domin su shahidai mutane ne na musamman wadanda Allah ya samar da su don yin ayyukansa na musamman .

Bari dai muji abinda Allah da Manzonsa (S.A.W.W )suka fada game da shahidai.

An karbo daga Masruq yace, ‘’ Mun tambayi Abdullahi Bn Mas'ud game da wannan aya;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KADA KUYI ZATON (cewa )WADANDA AKA KASHE A HANYAR ALLAH MATATTU NE, A'A RAYAYYU NE, S WAJEN UBANGIJINSU ANA CIYAR DA SU .‘’

  (AL-IMRAN:169)

Sai (Abdullahi Bn Mas'ud )yace, mun tambayi Manzon Allah ma'anar wannan aya , sai yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ Ruhinsu yana nan cikin cikin kurayen tsuntsaye (inside some green birds ), tare da su (tsuntsayen )akwai wasu fitilu (lanterns )dake lanqaye a jikin al'arshi , suna yin shawaginsu duk inda suka so cikin Aljannah . Duk inda suka zaga sai su dawo jikin wadannan fitilu (as their shelter ).

Wata rana sai Ubanjinsu ya kalle su yace;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ SHIN, AKWAI WANI ABINDA KUKE SHA'AWA NE NA DABAM ?‘’

Suka ce, ‘’ Wanne irin abu ne kuma za muyi sha'awarsa ? Alhali muna yin shawaginmu cikin  Aljannah ta duk inda muke so?‘’

Sau uku Allah na yi musu irin wannan tambaya (the same questions ). Yayin da suka fuskanci cewa ba za a bar yi musu tambayoyi ba (don qaunar da ake yi musu ), sai suka ce;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ Yaa Ubangiji! Muna buqatar ka dawo mana da ruhunanmu cikin gangar jikinmu wanda hakan zai bamu dama (mu dawo duniya )a qara kashe mu !‘’

Yayin da Allah ya fuskanci babu wani abinda suke sha'awa koma bayan abinda ya yi musu, sai ya barsu .

(Bukhari ne ya riwaito ).

AMINCI YA QARA TABBATA A GARE KA YAA

          ISHAQ

               M
               U
               H
               A
               MMAD

          SULAIMAN  !

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da  Ado  Isah  Guda.

          08126385470

~14th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post