shifa maqiyinka baya ganin duk want alheri naka Koda yagani zai kauda idon sa


Qasar Amurka ta kasance qasa mafi tsananin qiyayya da nuna makirci ga muslimci da musulmai , sannan kuma ta kasance abin tsoro ga qasashen duniya .
Babu irin barazanar da ba ta yi kan musulmi da kuma neman bautar da su kamar bayi. Hakan kuwa ta faru ne 





sakamakon ganin qarfin makamai da take da su har tana gani kamar mulki da ikon duniya na hannunta ne.
Tana yin amfani da qarfin tattalin arziqinta wajen mamaye qasashe ta hanyar ba su bashi, hakan kuwa kan sa qasashen su zama 'yan amshin shatanta , duk abinda tace sai suce daidai ne, ko da kuwa munin abin zai iya sanadin rushewar duniya.
Bisa iko da qarfin Allah sai ya sanya qasar Iran ta kasance mafi tsananin kishin muslimci da kuma aikata shi a aikace . Wannan baiwar da Allah ya yi musu sai suka zama barazana ga kafircin duniya , har ta kai qasar da ke ganin kanta a matsayin Giwa wacce kan iya take komai da kowa na tsoron ta.
Abinda ya soma faruwa yanzu tsakanin wadannan qasashe biyu ya soma bayyana izzar muslimci a duniya baki daya.
Sai dai abin takaici shine, maimakon musulmi su yaba musu tare da nuna murnar cewa za su sami 'yanci sai ya zamawa wasu musulman na aibantata don qiyayya.
Abinda suke cewa shine, wai IRAN tana kashe musulman IRAQI . Har ma wasu na cewa ai babarodo ne kawai, domin aiki ne iri daya suke yi da Amurka.
Cikin sukar da suke yi akwai cewa wai sun hada baki ne da Amurka don su kashe mutanen Iraqi Ahlus-Sunnah , wai saboda kowa in ya tashi kai hari cikin Iraqi zai aika.
Suna qarawa da cewa wai in ba tsoro ba me yasa Iran ba za ta kai harin nata kai tsaye zuwa Amurka ba? Sun manta da cewa suma Amurkan ba kai tsaye suka kai hari cikin Iran din ba.
Gaskiya maqiyi bai yi ba a rayuwa, domin ba ya ganin dukkan wani alheri naka .
ALLAH KA RABA MU DA MAQIYI NA ZAHIRI DA BADINI!

Tare da Ado Isah Guda .
08126385470

~13th January , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post