Ruwayoyin Dake tabbatar da Kona Gidan Sayyada Fatima 'Yar Manzon Allah (S)!!



➝MJ Matashi Ibrahim

___________________

-Maganar sanya wuta a wannan babban gida, gidan Sayyada Fatima da Imam Aliyu (As) lamarine wanda babu tantama a cikin aukuwar sa, kamar yadda Malaman tarihi daga ko wanne sashe suka ruwaito aukuwar sa.

-Bama kawai sanya wuta a wannan babban gida ne Malumma suka ruwaito ba. Mashahurai daga cikin littafan tarihi na magabata sun ruwaito batun dukan da akayi wa Sayyidah  Fatima (As), wanda hakan har yayi sanadiyyar barewar cikin da take dauke dashi a wannan lokacin.

-Wannan kuwa duk ya faru ne bayan abin daya gudana a Sakifa .

-Akan wannan magana Malaman Ahlus Sunna daban-daban sun kasa aminta ko kuma in ce suna nuna hakan baima aiku ba ne.

-Wasu daga cikinsu suna ganin batun cewa an kona gidan Sayyidah Fatima (As), bawani mugun aiki bane da har za'a iya sukan Khalifa ko kuma shi Umar da ruwayoyi suka zo da cewa shine ya jagoranci aikin kona gidan Nata.

-A cewar su idan ma har akwai laifi a kan wannan aika-aikan to bai wuce ire-iren kananan laifukan nan ba daza a iya kauda kai a garesu, domin kuwa ai babu laifin a kansa don ya ladabtar da wanda yayi wa zababben shugaba tawaye a cewar su.
Wa iyazubillah!

-Daga cikin Malaman na Ahlus Sunna akwai masu cewa, sam wannan lamari na an kona gidan Sayyidah Fatima (As) karyane, hakan ma sam bai faru ba, kirkira ce kawai daga 'yan Shi'a domin su illata Abubakar da Umar.

-Kuma can cikin littafinsu mai suna "Tamhid" a kan sharhin Muwadda Malik Mujalladi na 8, Shafi na 16. Sun ruwaito duba don ganin yadda suka yi ta sassabawa da kuma bayar da fahimtocin su a kan wannan magana.

-A nan dan abin da muke kokarin yi shine; dan rairayo wani abu daga cikin abin da wasu daga cikin mashahuran ma ruwaita tarihi daga cikin Malaman Ahlus Sunna  suka ruwaito a cikin mashahuran littafansu.

-Ta kuma hanyoyin dogaro da sahihai kuma ingantattun, muna kuma yin hakan ne domin kara wayar wa da mai karatu gaskiyar abin da ya faru a wancan lokacin.

-Ruwayoyin suna da yawan gaske, ta yadda ba zai yuwu ba akawosu lokaci daya ba.

-Zamu fara insha allah da wannan ruwayar sannan zamu ke kawo wa da kadan-kadan.

RUWAYAR IBN ABI DARA'AM

~Tabbas Umar ya naushi Fatimah(as)har saida hakan yayi sanadiyyar zubewar cikin Muhsin Danta"

~Za'a sami wannan ruwayar a wurare kamar haka:·

Sayru A'alamil nablah, Mujalladi na 15, Shafi na 578.
Mizanul I'itidal, Mujalladi na 1, Shafi na 139.
Alwafiy bil Wakiyat, Mujalladi na 6, Shafi na 17.
Lisanul mizam, Mujalladi na 1, Shafi na 406·

RUWAYAR SAFADI
~Umar ya shuri cikin Sayyidah Fatimah (as)a ranar da ake neman mijinta da abokanan sa suyi mubaya'a, wanda hakan shine yayi sanadiyyar barewar cikin Danta Muhsin."
Al-Wafibil Wafiyat, Mujalladi na 6, Shafi na 17·

INSHA ALLAH IN YANAYI YA BADA ZAMUCI GABA

DAGA
@MJ' Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@gmail.com

Masha Allah😭

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post