🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update
_____________________
_Da Sunan Ubangiji Mai Daukaka a Dalai Tsira Da Aminci Sutabbta Ga Annabi Muhammad Da Iyalai Tsarkaka.
RUWAYAR AL-JUWAYNI AL-SHAFI'I
_Ya fitar da wannan cikin wani hadisi mai tsawo ta hanyar Ibn Abbas, Ma'aikin Allah(S) yace;"Dangane ko da diyata Fatimah, a duk lokacin dana ganta, (Fatimah AS)nakan tuna abin daza ta gamu da shi a bayana. Ina ganin cin mutunci a yayin da yake shiga cikin gidanta, yan keta mutuncinta, da kwace mata hakkokinta da hana mata gadonta, da karya mata awaza, da sabbaba mata yin barin cikinta, a lokacin da take kira da;Ya Muhammad ! alhalin babu wani mai amsa mata. Za ta nemi taimako, amma baza a taimaka mata ba. Zata kasance a cikin matsanancin bakin ciki a bayana, kuma kullum a cikin kuka da bacin rai.
_Domin karin bayani sai aduba cikin;.
_Sadaruddin Abul Mujami'i, Ibrahim Ibn Muhammad Ibn Mu'ayyid Al-Juwainy Ash-Shafi'i, cikin (Fara"idus Simtayn), Mujalladi na 2 shafi na 34, yana daya daga cikin manyan malaman zahabi, a zamaninsa da yawa daga cikin mutanan Iraki , Sham, da Hijaz duk da shi suke dogaro.
RUWAYAR IBN KUTAIBAH AL-DAINURI
_Ya ruwaito cewa;"sai Umar yace a kawo masa makamashi, sannan yadaga muryarsa da karfi yana cewa mutanan dake cikin gidan nan, na rantse da Allah, wanda raina ke hannunsa, matukar baku fi toba, zan kona gidan nan. Sai wani yace ya baban Hafsat, Fatimah fa tana cikin gidan!" Sai Umar yace;to sai me?! Wannan bai dameni ba, koma waye acikin gidan.
_Domin Karin Bayani Sai Kaduba Cikin Wannan Littafin;Al-Imamah Wal-siyasah,Shafi na 12.
INSHA ALLAH ZAMU TSAYA ANAN ZAMUCI GABA
Masha Allah 🙏
Daga Wakilinmu Na Kano
MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com
KUKASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH DOMIN ILIMAN TUWA DA KUMA SANIN YADDA DUNIYA KECIKI.
Tags:
Taskar ilimi