Ruwayoyi Dake Tabbatar Da Kona Gidan Sayyada Fatimah 'Yar Manzon Allah (S) !! Kashi Na Uku (3)



🇳🇬Ma'asumah Nigerian News Update

____________________

Da sunan Allah Mai Firgita Azzalumai Tsira Da Aminci Su tabbata Ga Annabi Da Ahalin sa Tsarkaka.

RUWAYAR DABARI

_Daga Ibn Humaid daga Mughira daga Ziyad bin Kulaib, "Umar bin Khattab yazo gidan Ali, Dalha da Zubair da wasu Muhajirun duk suna cikin gidan. Sai Umar ya daukaka muryar sa da karfi yana cewa;.  "Narantse da Allah ko dai ku fito kuyi mubaya'a ko kuma nasan yawa gidan nan wuta.

_"Sai Zubair ya fito da takobin sa tsirara, sai kuwa yayi tuntube da wani abu, nan take sai takobin ya kubce daga hannunsa, shi kuma ya fadi kasa. Sai su kuma (Umar da jama'arsa)suka yi kansa suka damke shi."

_Domin karin bayani sai ka duba Littafin;Tarikhu Dabari Mujalladi na 9 shafi na 186 zuwa na 187.

RUWAYAR DABARI(2)

_"Ibn Humaid yaba mu labari yace Jurair ya bamu labari daga Mughirah daga Ziyad bin Kaleeb yana cewa;Ai daga nan (Sakifah)sai Umar ya nufi gidan Ali, wanda a lokacin su Dalha da Zubair da wasu Muhajirun duk suna cikin gidan (Na Ali).

_Umar ya daukaka muryar sa da karfi yana cewa; Ku fito kuyi mubaya'a, idan kuwa ba haka ba zan sanya wa gidan nan wuta. Sai Zubair ya fito da takobin sa ya nufi umar, amma sai kafarsa ta zame ya fadi kasa, takobin sa kuma ya kubuce daga hannunsa, ya fadi can gefe guda.

_Nan take sai mutanan Umar sukayi kansa sukai mai taran dangi suka cimimiyesa suka damke shi.

_Dan karin bayani shima kaduba;Tarikhu Dabari Mujalladi na 3 shafi na 202.

INSHA ALLAH ZAMUCI GABA
 
     Masha Allah🙏

Daga Wakilinmu Na Kano
@MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com

KUKASANCE DA SHAFIN MA'ASUMAH AKO YAUSHE DOMIN ILIMAN TUWA DA SANIN YADDA DUNIYA KE GUDANA

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post