Gidan Sayyada kenen |
Kashi Na Biyu(2)
⇀MJ Matashi Ibrahim
_____________________
_Dasunan Allah mai tukunkuna Azzalumai Nake farawa Tsira da Aminci su tabbata ga Annabi da Ahalin sa Tsarkaka.
RUWAYAR IBN ABDUL BARR
_Ibn Abdul Barr yace;Muhammad bin Ahmad yabamu labari,Muhammad bin Ayub yabamu labari,Ahmad bin Amru Al Bazzar yabamu labari,Ahmad bin Yahaya yabamu labari,Muhammad bin Yasir yabamu labari,Abdullahi bin Umar yabamu laabari,daga Zaid bin Aslam daga Nabansa:Aliyu da Zubair sun kasance suna shiga wajen Fatimah Diyar Ma'aikin Allah(s),suna shawartarta.A lokacin da aka yiwa Abubakar mubaya'a,sai labarin hakan ya kai ga Umar,sai ya fita harya iske Fatimah (as).Sai yace mata;"Ya Diyar Ma'aikin Allah(s),(Na rantse da Allah)babu wani daga cikin halittun da yafi soyuwa a gareni fiye da mahaifinki.Babu kuma wani dayafi soyuwa a gare mu baya ga mahaifinki(s).To,labari ya iso gareni cewa wadannan mutanen suna taruwa a warinki.To,idan na sake jin labarin hakan,to zan aikata kaza da kaza."Bayan da Umar ya tafi sai suka zo,sai tace masu;Umar yazo mini nan yana mai rantsuwa da Allah(T),matukar kuka sake,zuwa zai aikata kaza da kaza.Na kuwa rantse da Allah (T)zai iya aikata kaza da kazan.
_Domin karin bayani sai aduba cikin Littafi mai suna;Isti'ab,mujalladi na 3 shafi na 975.
RUWAYAR MAS'UDI
_Ya ruwaito cewa;sun kaiwa gidan Aliyu hari, sun kona kyauran gidansa,suka fito da shi da karfin tsiya,suka matse Fatimah a jikkin kofar,har saida tayi barin cikin Muhsin danta.
_Karin bayani cikin Littafin;Isbatal-Wasiyya
INSHA ALLAH ZAMU TSAYA NAN ZAMUCI GABA
Masha Allah 🙏
DAGA
⇀MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com
Tags:
Taskar ilimi