Rashin Zuwan Al-kaliya Ya Jawo Sake Maidasu Gidan Yari Ayau Ku Karanta Kuji

GAME DA CASE DIN 'YAN UWA NA PRISON DIN KADUNA.

           17/1/2020.

By Ishaq Adam Ishaq Esq.

THE STATE
           VS
MAHADI MUNKAILA & 90 OTHERS.

Kamar yadda a ranar 5/12/2019 (na shekarar da tawuce)wanda a ranar ne yakamata kotun ta yanke hukunci,amma bata zauna ba, aka sanya yau(17/1/2020) domin yanke hukunci.

A safiyar yau din mun isa kotun, jim kadan sai aka kawo 'yan uwa. Kafin afara fito da 'yan uwa, sai aka sanar damu cewa, wai kotun bazata zauna ba. Wai ita mai Shari,a tayi bayanin hakan tun jiya. A iya fahimta ta, da kuma fahimtar duk wani mai lafiyayyen hankali,akwai makirci a lamarin. Domin case dinnan fa angamashi. Yanke hukunci kawai za,ayi. Kuma hukuncin ne ba zaiyiwa su El-rufa,i dadi ba. Shine dalilin kai. Shiyasa suke jan lokaci a kan hukuncin. Domin Wannan shine dagawa na biyu kenan. Angama yin case din. Babu wani abu da za,ayi sai yanke hukunci. Inhar kotu ta zauna,to yanke hukunci ne zatayi. Hukuncin kuma shine,sakin 'yan uwa zatayi. To hakanne su El-rufa,i basaso. Amma Komai nisan jifa,zai fado kasa. Kuma komai nisan dare,gari zai waye.

Daga cikin abubuwan da sukasa El-rufa,i bayasan 'yan uwa sufita shine, shi wannan case din yana daga cikin determining factor ne na case din su Sayyid (H),wanda yau saura kwanaki 20 dai-dai.

Sannan wani abu mai zafi kuma shine,muntafi ba tare da ansan ranar da za,adawo kotun ba. Wato an daga case din cinodie.  Domin kotun ce yakamata ta bayar da wata ranar,amma ba tayi hakan ba. Allah ka wargaza azzalumai da duk mai goyon bayan su.

Yakamata 'yan uwa sufahimci cewa,shifa El-rufa,i kasan tuwarshi mai ilimi kuma dan siyasa,yafi gane karatu da babban baqi. Irin wannan karatun zaifi ganewa,tunda shi mai ilimi ne.

Free Allamah Sayyid Ibraheem Zakzaky(H)

Via legal highlight & opinions.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post