Daga Abuja:/ Rahotannin da suka zo Mana daga birnin tarayya abuja

  • Rahotanni dake shigowa na nuni da cewa jami’an tsaron ‘yan Sandan Nijeriya sun afkawa yan uwa musulmai masu gwagwarmayar tabbatar da addinin musulunci wayan da aka sani da ‘yan shi’a masu muzaharar lumana don ganin an saki jagoransu, Shaikh Ibraheem Zakzaky a Abuja.
Masu wannan muzaharar dai yauma kamar kullum yadda suka saba, fitowa a kowace rana a yau Talata sun dakko muzaharar ne daga Sky memorial, inda suka nufi gadar Berger dake cikin birnin tarayya Abuja.
Munsa mu tabbsci daga Shaidun gani da ido sun bayyana cewa; ‘yan sanda sun harba tiya gas a yayin daga bisani kuma suka yi amfani da harsasai masu rai kan masu muzaharar. Inda bayanai daga bangaren ‘yan shi’ar suka ce an raunata musu mabiya biyar, a yayin da ya zuwa hada wannan rahoton ‘yan  sandan ba su ce uffan ba dangane da wannan lamarin.
Su dai masu muzaharar ne wanda mafi yawansu matasa ne, sun fito maza da mata, inda suna me kira da gwamnati ta saki jagoransu kamar yadda kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta nema tun cikin shekarar 2016.

mudansirbaraamalumfashi@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post