Dubun-dubatar 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy na Da'irar Kaduna da kewaye sun sake fitowa domin cigaba da nuna matsin lamba ga hukumomin gwamnatin Nigeria akan ta gaggauta sakin Sheikh Zakzakiy daga tsarewar da take masa na haramci, bayan da wata babbar kotu mai mazauni a Abuja, da mai shari'a Mr. Kolawale ke jagoranta, ta bayar da umarnin cewa a sakeshi da mai dakinsa Malama Zeenah, kana a biyasu diyyar tsarewar da akayi musu ba bisa qa'ida ba, tun a shekaru kusan uku da suka gabata.
Hukumomin kasar dai sunyi kunnen uwar shegu, suka sanya kafa sukayi fatali da wannan umarnin na kotu, a inda suka cigaba da tsare Shehin Malamin da mai dakin nasa ba bisa qa'ida ba,
A karshe gwamnatin jihar Kaduna ta sake gabatar dashi a kotu mai mazauni a Kaduna da wasu sababbin tuhume-tuhume na qarya da qarairayi marasa tushe da Malama.
Muzaharar ta neman ganin an saki Sheikh Zakzakiy ta gudana ne a kan titin Kaduna to Abuja express way, andai fara muzaharar ne misalin karfe 6:00pm, an farotane daga gwamna road junction aka rufe a bypass daura da masallacin Shehu Dahiru Bauchi.
An farata lafiya kuma an kammala lami lafiya.
-J.S.A
-M.N.U 016.
-17/01/2020.
Tags:
#FREE_ZAKZAKY