Mutum 14 Sun Rasa Rayukansu A Farmakin 'Yan Bindiga

Daga Wakilin Shafin Mu -Idishia Jos.

Kwanaki 3 da suka wuce Rundunar 'yan sanda a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutum 12 a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a kauyen Kumbel da ke Gundumar Kombun a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato.

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP, Mathias Tyopev, ya ce wasu mahara ne suka far ma kauyen.

A cewar Irmiya Datim, mutum 14 ne maharan suka kashe a kauyen, ya kara da cewa a yanzu haka mutane na kauracewa gidajensu, suna barin gari domin fargaba.

A jihar ta Filato, akan dai samu rashin jituwa a lokuta da dama tsakanin makiyay da manoma, batun da kan haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Sai dai tsohon sakataren kungiyar Miyetti Allah a jihar Filato, Abdullahi Ardo ya ce, ba su da masaniyar wadanda suka kai harin, amma ya roki jama'a da su kai zuciya nesa

Gwamnan Jihar Filato, a wata sanarwa da Simon Lalong ya fitar dauke da sa hannun daraktansa da ke hulda da manema labarai, Makut Macham, ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen ingiza wannan rikici.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post