Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.
Harin makamai masu linzami wani bangare ne na wani jan aiki a yakin idan Amurka ta rama harin ramuwa da Iran ta kai mata, a cewar majiyoyi masu danganta kalaman da wani babban kwamandan Iran.
Kamar yadda gidan talabijin din kasar Iran ya ruwaito, Amir Ali Hajizadeh ya ce ramuwar da ta fi dacewa kan kisan Janar Qasem Soleimani da Amurka ta yi shi ne a kori Amurka daga yankin.
Kalaman nasa na zuwa ne kwana daya bayan Iran ta harba wasu makamai masu linzami a wasu sansanin Iraki da sojojin Amurka ke zama.
Wannan ya zo ne a matsayin ramuwar kisan Soleimani da wani jirgi marar matuki ya yi a birnin Bagadaza a makon jiya.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana wasu sabbin takunkumi da Amurka ta kakabawa Iran a ranar Laraba, inda ya ce Iran “ta huce” bayan da ta kai harin makaman masu linzami.
Sai dai bai kuma yi batun sake daukar wani matakin soja ba.
Amma a ranar Alhamis, Mataimakin Shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya shaida wa kafar yada labarai ta Fox News cewa “a bisa umarnin shugaban kasa, za mu ci gaba da zama cikin shiri.”
A wata hirar da kafar CBS, Mista Pence ya ce Amurka na samun “rahotannin sirri masu karfafa gwiwa” cewa Iran ta aika da sakonni ga kungiyoyi masu goyon bayanta da cewa kada su kai wa Amurka hari.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian
Tags:
Labaran Duniya