Shafi Domin Al'umma.....
🇨🇮 Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bin Haroun Sigau.
Taqaitacen tarihin Dutsen.
Aqeeq wani dutse ne mai daraja da ake amfani dashi tun zamanin Manzon Allah (S) wanda yazo a tahiri ana samun sa ne da a wani kogin Italy da ake kira da Sicily amma anfi sanin kogin da Achetes River, wanda kuma a larabci ana kiran sa ne da Wadi-Ikrilu.
Lokacin da mutane suka gane wannan dutse sai suka fara amfani dashi wajen kwalliya da sanya shi ya zam suna tafiya dashi ko ina zasu tafi.
Dutsen Aqeeq yana da kaloli daban-daban amma wanda yafi ko wanne shine ake kira Aqeequl Yamani, a wannan zamanin mafi yawan cin abubuwan da aka fi yin amfani da Duten Aqeeq sune Yin Zobe, carbi, da kuma kayan ado na mata.
Amfanin Duten Aqeeq.
Dutsen Aqeeq yana da matuaqar amfani a Muslunci, zan iya cewa ma shi musumin dutse ne. Domin yazo a tarihi Manzon Allah (S) yana saka zobe mai dauke da wanna kalan dutse din.
Yana daga cikin amfaninsa ga mai saka zoben Aqeeq samun sanyi cikin zuciya da kwanciyar hankali.
Yazo a ruwaya daga Sayyada Fatima (S) tace, "Saka zobe mai dauke da dutsen Aqeeq yana karo arziqi, kariya daga baqin tsafi kuma zai zama kari ya gare ka daga maqiya.
Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi da iyalan gidan sa yace, "Duk wanda yake Sanya zoben Aqeeq zaike samun biyan bukatar dukkan abinda ya roqa.
Salmanul Farisi ya ruwaitoa a wani hadisi dake cewa; "Manzon Allah ya Bukaci Imam Ali ya rinqa sanya Zobe a hannun dama domin ya samu zama daga cikin Muqarrabeen (Masu kusanci ga Allah)".
Imam ya tambayi Manzon Allah su waye maqarrabeen? Manzon Allah yace, "Mala'ika Jibril da Mika'il". Sai Imam ya qara tambaya wanni kalan zobe zanke sakawa?
Manzon Allah (S) yace; "Dutsen Aqeeq domin jan Dutsen Aqeeq shine dutsen daya yarda da dayantuwan Allah da Manzon karshe da iyalan gidan sa, hadi da wasiyyin sa Ali Bn Abu Thalib".
Imam Ali (As) yake cewa, Ku saka zoben Aqeeq zai zam mai yaye muku baqin ciki.
Yazo a ruwaya daga Imam Jafar As-Sadiq (As) yace, " Sallah tareda zoben Aqeeq yafi sallah sau arba'in (40) ba tare dashi ba.
Imam Muhammad Baqir (As) yake cewa, "Da mutum zai sai zoben Aqeequl Yamani ya kalle shi tare da Karanta Suratul Qadar, zai zama cikin kariya baki dayan yinin ranar.
'Yan uwa kada wani daga cikin yazam yana itiqadi da bin wannan gidan na annabta ba tare daya mallaki wannan zobe ba, hakika akwai gayar muhimmanci ga sanya shi.
Tags:
Taskar ilimi