Mijina ne ya tilas ta mani bin Maza.

Daga Wakilin mu --Idishia Jos.

A ranar Larabar nan ne wata mata mai sana’ar gyaran gashin mata, Opeyemi Bakare, ta shaida wa kotun al’ada da ke Mapo da ke Ibadan cewa, mijinta da su ka shafe shekaru 13 su na zaman aure da shi ne ya tilasta ta bin wasu mazaje su na lalata da ita a bisa yawan qorafinsa da kuma barazanar da ya ke yi ma ta.

Da ta ke bayar da shaida a gaban kotun, Opeyemi Bakare, wacce ke zaune a Unguwar Olunde, Ibadan, ta shaida wa kotun cewa mijin nata Olawale, yakan lakada mata shegen duka.

Tabbas, ina bin wasu mazajen muna yin lalata. Da farkon lamarin dai a duk lokacin da wani namiji ya nemi na ba shi lambar waya ta, nakan ba su lambar wayar mijin nawa ne saboda su daina matsawa suna bi na. To amma, a lokacin da Olawole ya canza dabi’arsa a gareni, ya zamana ba ya saurara mani, sai ya zamana tilas a gare ni da na bi wasu mazajen wadanda za su kula da ni da kyau, wadanda kuma ba za su bar ni a cikin Yunwa da qishin ruwa ba.

Danna Jan Rubutun Domin samun rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga


A lokacin da mijin nawa ya gano cewa ina bin wasu mazajen, sai Olawale ya kwara mani fetur da nufin ya qyasta mani wuta na qone qurmus da raina, amma sai Allah bai ba shi sa’ar ganin ashanar ba a wannan lokacin, da ya gani, da a yanzun haka sunana matatta ne. Sannan kuma sam ba ya ganin qimar mahaifiyata.

Da mijin yake kare kansa a zargin da matar na shi ta yi ma shi, ya musanta dukkanin zargin da ta yi ma shi din. Sannan kuma mijin ya qi amincewa da a raba auren na su. Ta faye qorafi, takan kuma zage ni, takan kira ni da duk abin da ta ga dama. Na kuma sanar da iyayenta munanan halayen nata. A koyaushe nakan tabbatar da na ba ta abin bukatarta ita da yaran mu uku. Ko don saboda ‘ya’yanmu ina roqon kotu da kar ta raba wannan auren namu, in ji Olawale.

Amma a bayan da alqalin kotun, Cif Ademola Odunade, ya gama sauraron dukkanin shaidun na su ne sai ya raba auren a nan take, a bisa hujjar cewa akwai barazana ga rayuwa a cikin zaman auren na su. Alqalin ya kuma bayar da renon yaran uku a hannun matar, sannan
ya yi umurni ga mijin da ya riqa baiwa matar naira 15,000 a kowane wata a matsayin kudin alawus na ciyar da yaran uku, baya ga haqqin daukan nauyin ilimin su da duk wani abu na jin dadin yaran da alqalin ya dora wa mijin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post