Matsalolin Zamantakewar Aure!!!


In aka kalli aure da idon basirar da kuma yacce yazo mana, zaka ga wani babbar nauyi ne wanda a addinance matuqar kasan baza ka iya sauke wa ba, kuma zaka iya kare kanka daga zina to bai zamo dole saika yi ba.

Amma abin duba anan shine menene ke haifar da yawan rabuwan aure da matsaloli a cikinsa?.

Abubuwa ne masu saukin ganewa da kiyayewa, ga mutumin da ya kalli aure a matsayin ibada zaifi mai sauki ya iya kiyaye su, amma inka dauki aure a matsayin kawai kana yi ne don sha'awe-sha'awe lallai kiyaye war sai a hankali.

Matsala ta daya: Karya yayin neman aure. Wannan yana faruwa ne tun farkon neman mace wanda a zahiri kai ba haka kake ba, amma kazo wajen yarinya kaita mata karairayi da abinda baka dasu.

Sai yarinya tazo gidan ka zaman aure taga hidindimun da ada kake mata yanzun kokwatansa baka yi mata.

Matsala ta biyu: Rashin Hakuri. Rashin hakuri ga maurata yana iya haifar da matsalar da ba'a tunani domin ita zuciya bata da kashi muddin ba za'a ke hakuri da juna ba dole ake samun matsaloli.

Domin shi zaman aure ana so duk lokacin da wani ya hau, wani ya sauka ne, in matarka ta daga murya kai kuma ka saukar, ka kaskantar da kanka ka rarrashe ta domin su dama sun fimu rauni.

Matsala ta Uku: Rashin sauke nauyin iyali. Wannan nauyi kuwa wajen abinci ne ko sutura ko kaya na yau da kullum, a duk lokacin da ka ga wata mace ta  fara daina ganin kimar mijinta zaka ga bai iya sauke hakkin sa ne akanta, domin mata sun fimu hakuri da juriya akan al'amura.

Amma inhar zai zamana matar ka bata gane samunka da rashinka, kullum kana cikin babu, abinda ya kamata kai mata inta tambaya kace; babu to, fa matsala ta dinga faruwa kenen.

Matsala ta Hudu: Yiwa yaran da basu gama mallakar hankukansu ba aure; wannan janibi ma babban lamari ne domin su kansu zasu iya lalata auren su ba tare da sun sani ba, kuma zaka ga abu kadan zai ke sakasu fada.

Wanda in ace mutumin da yasan duniya ne da yadda kuma ya mallaki cikakken hankali cikin sauki zaka ga sun zauna sun gyara kansu, amma su abu kadan zai ja a dauko kalamar rabuwa, da maganganu mara sa dadin hakan yakai ga furta abinda ba'a so.

Mastala ta biyar: Matsalar zama gidan yawa. Wannan matsalar tana tasiri matuka, mafi a kasari ta bangaren mace, yan uwanta mata zasu iya ingizata ga wasu munanan dabi'un da kai da baka san dasu ba.

Wanda in abin ace kuna gida daga kai sai itane zaka ga komi naka anfi tattalin sa kai kanka kafi nutustuwa da kadaita da ita, da faranta mata.

Bugu da kari tarbiyyar yaran ku, zai zama ba wasu shakiyyan yaran da zasu ke warware muku tarbiyyar yaran ku.

➡Fatan yayenmu, yayyen mu da Abokanmu zasu yi  amfani da wannan yar hasashe tawa su kula da iyaylin su yadda ya dace.
Allah yasa mu dace ya bamu zuri'a ta gari. Ilaheey

Daga Wakilin mu
Bin Haroun Sigau.
08065008703

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post