🇨🇮 Ma'asumah Nigerian News Update, tare da Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ.
Wannan lokaci ne da muke samun shigowar abubuwa daban-daban daga wasu al'ummu, muna wani zamani wanda abinda yake a nisan duniya yana shafan wasu kasashe.
Kamar abinda ke a kafafen watsa labarai, tauraron dan Adam da Internet sabida haka yanzu tarbiyyan mutane wani abu ne dake samun tasiri nan da nan.
A ko wacce al'umma takan dauki matakai na ganin cewa ta kare tarbiyyan mutanen ta. To, mu nan sai aka barmu kamar wawi, a sake kawai ba wata kariya yaran mu ba wata kariya da suke samu daga kutsowan al'adu da sauran abubuwa daga waje ta hanyar tauraron Dan Adam da fina-finai na yammacin duniya da sassa daban-daban.
Zamu ga Ainihin tarbiyoyi yana ta tabarbarewa, ta yadda nan gaba bamu san wacce irin al'umma zamu zam ba, wato wannan wani abu ne daya rataya akan ko wanne ta dukkan janibi na rayuwa baza'a ce samari kawai ba ko iyaye kawai ba, ko kuma malamai kawai ba, ko shuwagabanni kawai ba, duka ne za'a hadu ko wanne ya bada irin tasa gudunmawa din.
Don ganin cewa ainihin an kyautata tarbiyyar al'umma, hakan ya saka su samari sun dauka basu da wani kaya da bazasu dauka ba, komi kawai dauka suke, nan gaba bada jimawa ba zamu ga al'adun mu sun nemi su bace.
Sabida haka maganin wannan shine iyaye su riqa sa ido suna lura da me 'ya'yansu suke gani a television, me suke dubawa a internet, mene suke karanta wa, dawa suke hulda??
In su kiyaye zaka hana su duk wani huldodi amma zaka kiyaye kaga anyi amfani da mai kyau, domin waɗannan kafafe suna tattare da miyagun abubuwa a lokaci guda kuma suna da abubuwan kirki.
Kana iya kokari kaga cewa kana lura da abubuwan da 'ya'yanka suke yi, janibin iyaye kenen. Sai kuma Malaman makarantu su gane cewa; ba karantu a aji ne kawai aikinsu ba a'ah tarbiyya ne aikin su, domin shi tarbiyyan yaro ba da ka cusa mishi karatun shikenen ba.
A'ah ta ko wanni janibi ne, wajen sashin malamai kenen janibin karatu. Malaman addini su kuma wajibi ne su lizimci wa'azuzzuka sawa'un wajen tarurruka ne ko kuma masallatai ne, in kuma kiristoci ne a coci na.
Duk dai ana kokarin kwakkwafe tarbiyyan mutane ne, sai su kuma shuwagabanni lazim ne suyi aiki domin sanya kariya. Nai mamaki a wannna kasar bamu da wani kariya daka shiga zaka iya ganin komi a internet, amma a wasu kasar ka nemi ka shiga wani bangare a net zai nuna maka bazai yiwu ba, amma ku anan ko ina ana iya shiga ba mu da kariya irin wannan.
Naji ance akwai plan din za'ai doka wadda za'a rufe wasu site na internet musamman masu nuna abubuwan batsa ɗin nan, wannan abin ai marhaban dashi ne yakamata ace hukuma ita ma ta ɗauki matakai na ganin ta kiyaye tarbiyya kamar yadda tayi a dokar auren jinsi guda.
Hakanan kuma yakamata ta ɗauki matakai wajen tace irin abubuwan da zasu shigo mana da fina-finan da ake nunawa, wannan kuma hakki ne daya rataya a wuyan su. Sai kuma wanda koda yaushe kai ake hankoro ake kokarin a lalata, wato matashi, to, shima matashi shi ya kamata yai ma kansa kiyamul laili ka gane cewa; in ainihin duk ba'a taimake ka wajen kare kanka ba aka barka ka lalace to, ba wanda yafi cutuwa sai kai.
Sabida haka kai kar ka yarda ka lalacen koda kayan lalace wa sun ke waye ka ta ko wacce hali, kaima kanka kiyamul laili ka duba kaga wanni dattijo kake son zama anan gaba? In ka ga dattijon kirki to dama yaron kirki ne sai ya zama dattijo, inko kaga tsohon banza ka tabbata yaron banza ne ya sami ci gaba.
Domin ba yadda za'ayi ko a tatsuniya ce ake yi baka ji an taba ce maka; "Gatanan-Gatanan ku wata rana ne aka sami wani yaro mutumin kirki ya girma yana yaron kirki ya zama saurayin kirki, ya zama dattijon kirki amma daya tsufa ya zama lalataccen Tsoho"
Bazai taba yiwuwa ba, in dai kaga mutum a lalace to, ya bannatar da lokacin sa a lalace ne. Kai kanka kaima kanka fada, kai kokari kayi abinda shi zai amfane ka anan gaba din ka da ma makomarka lahira, domin akwai wani wahayin shaidan da yakan yi ma samari cewa; idan sun girma ne zasuyi addini.
To, ba idan an girma bane ake addini ba, ana yaro ne ake addini don lokacin da kake yaro ne kake majiyin karfi in ka bari ka tsufa ba wani addini da zaka yi, yanzu ne za'a ganka mutumin kirki ansan cewa za'a ga dattijon kirki ne wannan kuma dai fadakarwa ne, muna fata kuma zamu amfana.
—Allama Sayyid Zakzaky (H) a wata tattaunawa da aka taba yi dashi, shekarun baya.
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky