Mai zai hana ko wanni Mabiyin Zakzaky ya damfaru da ayyuka irin na Qaseem Sulaimani!!


➝MJ Matashi Ibrahim

_____________________

-Amincin Allah ya tabbata ga ma'abota wilaya da gidan annabta.

-Kamata yayi ace daga ranar da Allah ya dauki Sulaimani ace dukkanin dan Shi'a da mai hanqoro da goyon bayan gaskiya dake Nijeriya zai zama sanfuri kuma ma kwafi wajan aiki domin Allah tare da taimakawa Jagoran hanyar Gaskiya Sayyid Zakzaky(H).

-Muna ta jinjinawa Qaseem Sulaimani, amma mun kasa yin aikin da shi Qaseem yayi ya samu wannan shaidawar a gurin Jagoransa akan muma namu Jagoran.

-Menene amfanin alkawarin da muka yiwa Allah akan Sayyid?? Ko dama a iya bakin mu ne banda zuciyoyin mu?? Ya kamata mu koma ga aikin dake gaban mu dan muma mu rabauta kamar Qaseem.

-Ba laifi bane ka dinga yaban Qaseem Sulaimani, domin ko baka yabe shi ba manyan bayin Allah sun yaba masa kuma ya cencenta ne. Amma kuskure ne ka kasa aikata aikin dashi kasim ya aikata awannan zamani, domin shima mutum ne kamar kowa, bambancin kawai shine shi ya sadaukar wa addini ne kansa.

-Daukaka ambaton Qaseem Sulaimani babbar dama ce a garemu domin hakan zai taimaka mana wajan isar da sakon Maulana Sayyid Zakzaky.


-Kowa in yazam kamar Qaseem Sulaimani tabbas Sheikh Zakzaky zaiyi alfahari da hakan.  Amma in muka gaza zama kamar Qaseem gaskiya saidai muna ji mana gani ayi addinin bamu. Matsawar muna sin 'yanci to jajircewa shi zai sama mana 'yanci.

-Daga yau kaima ka  zama Qaseem, nima inzama Qaseem kuma ku zama Qaseem  ba'abakiba aiki, kaga Duniyar baki daya Sai ta zama Qasimomi kamar yadda muke amsa Husainawa, to, ga wani mai aiki irin aikin da ya kamaci Husainawa mu bada rai don tabbatar addini.

'Yan uwa kar mu dauka Qaseen din nan kawai soja ne da ake bamu labarin irin su a Nijeriya yaje yayi yaki shikenen, a'ah shi wannan mayaki ne wanda ya yaki zuciyar sa, kana ya yaki kafiran duniya masu muzgunawa bayin Allah.
Wannan aikin da yayi tsawin rayuwa shi ya kaishi ga wannan babban matsayi..

Muji, mu saka a zuciyoyinmu daga yau muna so mu zam Qaseem Sulaimani a aiki da cikawa.

@MJ Matashi Ibrahim
07032680713
matashi1234@email.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post