Ma'asumah Nigerian News Tayi Rashin Wakilin Shafin ta A Cikin Daren Nan.

Shaheed Ishaq Muhammad Sulaiman.

Tare da Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.

Innalillahi wa'inna ilahirraji'uun!!!

Yanzun nan labari yake zo mani cewa dan uwa Is'haka Muhammad Suleiman ya yi Shahada.

Daya ne daga cikin yan uwan da jami'an tsaro suka harba a hannu har dan yatsan sa ya fita a ranar Jum'ah 27/12/2019 a gurin muzaharar neman a saki Sheikh Zakzaky a Sakkwato.
Kuma ya rasu ne a sanadiyar wannan harbin da aka yi masa.
Za a yi jana'izarsa a gobe Assabar 11/1/2020 a garinsu Birnin Tudu, Mafara, karfe 11 na safe.
Muna fatar Allah ya karbi shahadarsa ya gaggauta daukar mana fansa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post