KU SADAUKAR DA DUKIYOYINKU A TAFARKIN ALLAH

A cigaba taron yan uwa almajiran Shaikh lbraheem Yaqoub Elzakzaky (H) Ahul Ahl-Dhthour suka fara gudanarwa tun jiya taron karawa juna sani mai taken *Zakka Da Khumusi* wanda aka baje kolin karatttuka daga malamai mabanbanta na harkar musulunci irin Sayyeed Badamasi Yaqoub, Sheikh Abdulhamid Bello, Sheikh Adamu Tsoho Jos, Farfesa Abdullahi Danladi, Farfesa Isah Maishalgaro, Sheikh Shuaibu Qum, Sheikh Abdurahaman Yola, Malam Tarmizh Kaduna, da sauran manyan malamai da Yan kasuwa na garuruwa daban daban.

A yanzu haka shaikh Yaqoub Yahya Katsina ya fara gudanar da jawabin rufewa, a  wani bangare na jawabin nashi yana mai kiran yan kasuwa da su kasance masu gaskiya da rikon amana, domin abunda mutum yace na halas shi ne abunda zai haifar ma'ana iyalinshi Kenan, idan aka ciyar da su halas zasu kasance na gari, idan aka samu akasin haka to mutum ya zargi kasanshi da abunda yake aikatawa.

Ya cigaba da cewa a guji yin rantsuwa a kasuwa ko da akan gaskiyar ne, domin rantsuwa tana rage mutum wani lokaci takan zama matsala ga mutum.

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 


Gaskiya ita ke zama ado da cigabantar da mutum, duk wanda aka yi kasuwa da shi ya kasance an gudanar da kasuwar bisa gaskiya da rikon amana yake, irin wadannan zaga cewa suna kawo wasu ma saboda an yi kuma sun ji dadi.

Wani lokaci ana irin wannan cinikin ya zama mutum yazo sayen kaya kun kammala cikin sai yaje gida matarshi ta haihu ko rashin lafia, ko wata matsalar da za'a mai do abunda aka saya, wasu Yan kasuwar basu badawa abunda suka dauka an gama cikin lallai hakan bai kamata, in haka ta kasance abunda ke naku maidawa mutum yaje ya yi bukatarsa, yin haka kuma ba karamin matsayin bane da lada gurin Allah da Manzonsa (S)

Allah Ya umarcemu zuwa Makka da Umra amma bai kamata mutum yaje Umra ba amma akwai ayyukan da suka kamata ya yi bai yi ba misali ace makarantar Fudiyyah ba shimfida ko filista babu mutum ya wuce wannan ya tafe Umra lallai wannan bai dace ba kuma ba dai dai bane.

Ku sadaukar da abunda Allah Ya baku wajen saboda Allah da Manzon, ku rika kyauta tana kara soyayya, ku sadaka ga misikinai marayu da fakirai, ko ace makarantar Fudiyyah kaje wanda yazo na daya zaka bashi abu kaza yin wannan taimakon addini ne, ko kuma mutum yace in Allah ya fito da Malam lafia zan ba mu'assasa kyautar million biyar, hanya wadda Allah ke ba bawansa wajen aikata alkhairai.

Sarrafa dukiya wajen aikin Allah ibada ce babba, wadda mutum yana iya kansa gini ne zuwa ga Allah (S) kuma yin haka yana cigabantar da rayuwa da yi mata albarka tare da koyawa al'umma ayyukan alkhairai, lokaci guda kuma ana da'awa ga koyarwar ALhul baity (AS) da cigabantar da kiran Maulanmu Shaikh Sayyeed lbraheem Yaqoub Elzakzaky (H).

Sannan kuma ina iya cewa ayyukan da ok idan muka kalli kawukanmu zamu ga cewa kowane mutum yana yin bakin kokarinsa misalin fara daga malamai ko wakilan yan uwa na garuruwa zaka ga cewa suna yin bakin kokarinsu sannan kuma in ka dubi bangaren Harisawa kana iya cewa komai sune sun sadaukar da komai, wani lokaci nake cewa wai wadannan Harisawa da nake gani kullum su basu da wajen kwana ne aka cemin harma suna da mata, amma zaka ga cewa kullum suna nan.

Idan muka dawo bangaren yan Ahul douthor muna iya cewa lallai basu yin abunda ya kamata ba, ya kamata ace idan Sayyeed (H) ya dawo ya tarar da katuwar katafariyar sakatariya da kuka Gina, idan muka kalli Hisbullah zamu ga cewa a sani bangaren ( mu'assasa) ana yawo da abun baki dayansa a jikka amma yanzu sakatariyarsu ko ta Abuja ba ta kai ta ba.

Mu sani cewa wannan aikin abunda ya shafi Fudiyyah da sauran abubuwan harka kowane bangare kune zaku yi, ku sani wannan abun fa shine ke taimakonku shi ke cigabantar da arzikinku da dukiyarku gaba, shi zaku yi idan Sayyeed (H) ya ji dadi ya kara saka maku albarka dukiyarku ta wuce inda ake zatonta saboda sadaukarwa ga Allah da Manzonsa ( S)

Akwai kuka bangaren Tablig yana da kyau mu kara shiga kauyuka domin cigaba da koyar da al'umma Kiran Manzon Allah (S) da iyalansa tsarkaka (AS) da kuma jagoranmu domin wannan aikin shine abunda yake shekara 40, mu shiga kauyuka domin kauda wulayar da mutanen kauye suke yiwa hakimi da shugaban yan sanda, ace kashi 50 mutanen kauyuka bi Malam.

Daga karshe mu ina baku shawarar mu samar da wani kasuwancin da namu ne, ace yau ga wani abu in ba wajen Yan shi'ah ba'a samunshi, kamar Sayyeed (H) yake koya mana cewa mu samar da kasuwanci na bai daya, misali kiwo da noma ko kuma mu samar da ruwa domin al'umma kowa yasan dai halin da ake ciki a ciki na matsalar ruwa.

Ku guji halin Yan kasuwar na rashin kyautata wadanda ake mu'amula da su, misali ace kuna aiki da mutum amma ba'a biyan mutum lokacin da ya kamata yin haka yana durkusar da mutum, yazo a hadisi duk wanda yake zaluntar yaronshi ko Lebira Allah Ya la'anceshi, ya kamata ace akwai lokacin fara aiki da na gamawa sannan kuma akwai kari lokaci lokaci hakan kuma ya danganta da abunda ake samu, idan kowanemu ya kasance haka mu cigabantar da harka da kiran Maulanmu.

Daga karshe kowane bangare muyi kokarin yin abunda ya kamata yadda in Sayyeed (H) ya dawo zaga cigaba ne maganar matsaloli duk sun kwarenye, ya kamata duk inda mutum ya samu kanshi yace kokarin yin aiki dan Allah da cigaban kiran su Malam.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post