Kisan 'Yan'uwa Musulmi A Abuja Ya Sabawa Dukkan Dokoki – Inji Sheikh Halliru Maraya....

Kisan 'Yan'uwa Musulmi A Abuja Ya Sabawa Dukkan Dokoki – Inji Sheikh Halliru Maraya....                         🇳🇬                    Ma,ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE 🇳🇬   👉BY SHARHABIL USMAN PANDOSS                         
Shaikh Halliru Abdullahi Maraya wani fitaccen Malamin Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, ya bayyana cewa, kisan da Sojojin Najeriya ke yiwa 'yan'uwa Musulmi ya saɓawa doka.
Shehin Malamin ya shawarci gwamnati akan da ta buɗe kofar tattaunawa ne da Harkar Musuluncin domin ganin an samar da mafita tare da samar da hanya mafi sauƘi wajen ci gaba da gudanar da muzaharori domin kaucewa rasa rayukan al’umma da dukiyoyi.
Malam Halliru Maraya ya bayyana cewa, "Kotu kadai take da damar yankewa ɗan kasa hukuncin kisa.” Inji shi.
A wani bangare na bayanin na shi Malamin ya yi, ya kara da nuna cewa manyan manufofin kowacce gwamnati shi ne, kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce, "Abin baƘin ciki ne a ce a wannan zamanin na ci gaba, muna ci gaba da kashewa da wulaƘanta gawarwakin matasa ‘yan Ƙasarmu. A lokacin da sauran Ƙasashen Duniya ke horas da nasu matasan domin samun Ƙwarewar da za su iya shugabanci a nan gaba".
A cikin wannan makon ne dai Sojojin Najeriya suka akawa ‘yan'uwa Musulmi a lokacin Tattakin Arba'een na bana a birnin Abuja, inda suka kashe mutane da dama sannan suka jikkita wasu, tare da kama sama da mutane 400.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post