➝Daga βιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ
🇨🇮 Ma'asumah Nigerian News Update.
Wadannan zantuka ne na Imam Ali (As) da aka kawo cikin littafin Gurar Al-hikima, dangane da mutuwa.
1- Duk lokacin daka kusanto mutuwa, ka kyautata ayyukan ka akan na da.
2- Ga dukkan lokacin da ake tsammani akwai ranar da za'a kai ga abin tsammanin.
3- Ga ko wanne mutum akwai ranar da zai tafi kuma bazai sake dawowa ba.
4- Ga ko wanne mutum akwai direba dake tuka shi zuwa ga mutuwarsa.
5- Inda zai zam ana ganin kusanto war lokacin mutuwa da kowa ya ringa tona dukkan sirrin sa.
6- Idan da zaga mutuwa tana kusanto ka, hakika, zaka tsani rikici da yin karairaku
7- Idanu zaka ke tunani akan kusancin ka da mutuwa, da tanar zuwanta. Jin dadi da wakwakar duniyar ka zai kau.
8- Duk wanda yake mai kiyaye wa da mutuwar sa, zai zam mai karancin tammani.
9- Wanda yaki daukar duniya madauwama, zai zamodaga cikin masu karancin buri.
10- Wanda ya kyautata ayyukan sa baida burin da ya fice mutuwa.
11- Wanda yake kirga gobe a matsayin cikin rayuwar sa, bai bawa mutuwa muhallin da yac da ita ba.
12- Menene maganin da yafi komi! Shine; mutuwa!
13- Babu garkuwar da ke bada kariya kamar lokacin mutuwa.
14- Babu abinda yake na gaskiya kamar mutuwa.
15- Kai abin gurbi ne, sabida an saka maka lokacin mutuwa, kuma mutuwa kullum haru take kawo maka.
16- Amincin Allah ya tabbata ga wanda ya gane dukkan kwallin numfashin sa yana kara kusanto dashi ga mutuwa ne, don haka yayi hanzarin kyautata ayyukan sa na gargaru
17- Rahmar Allah ta kara tabbata ga mutumin da ya karyata tsammanin sa, ya kuma kyautata ayyukan sa.
18- Wasu lokatun mutuwa takan buya karkashin tsammani.
19- Da shudewar awan ni, rayuwa ke karewa.
20- Hakika, akwai garkuwa gare ni, ta wajen batun mutuwa ta, in lokaci yayi garkuwar da kanta zata kauce ta bayar a dauki raina.
21- A wannan lokacin kibiya bazata kauce wa sauti abin hari ba, rauni kuma bazai warke ba.
Wa iyazu billah.😭
'Yan uwa mu gyara Alaqarmu da Allah domin mutuwa ba sallama take ba.
Allah ka kyautata karshen mu, kasa muzam cikin Shaheedan Karbala.