Jawabin Sheik Yaqub Yahaya na Rufe Muzaharar #Free Zakzaky a garin Katsina yau Juma'a 17/01/2020


A yaune Juma'a aka gudanar da Muzaharar neman Gwamnatin Buhari da ta gaggauta Sakin Malam Ibrahim Zakzaky bayan Sallar Juma'a, Muzaharar ta tashi daga Babban Masallacin Juma'a na garin Katsina zuwa Filin A.t.c a inda Wakilin 'yan uwa Musulmai Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky na Da'irar garin Katsina Sheik Yaqub Yahaya yayi Jawabin Rufewa ka kadan daga cikin Jawabin

Sheik yana cewa "mun ji daga bakin manyan kusoshin Gwamnati daban-daban sun cewa sungano babban kuskuren da Gwamnatin Najeriya ta tafka shi nee da ta taba Addinin Muslunci domi tsare Malamin 'yan Shi'a da akeyi bazaihaifar da komi a Kasarnan ba sai rishin kwanciyar hankali"

Sheik ya kara da cewa " Gwamnatin Najeriya gwamnatice ta Zalunci da taushe hakkin 'yan Kasarta da rishin sanin kimar 'yan adamtaka tsare Malam Zakzaky da akeyi abisa Zalunci, shuwa gabannin Kasarmu ta Najeriya basa nifin adalci ga Malam Zakzaky, Allah adali ne, Allah baya zalunci bayason mai Zalunci".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post