@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA CEWA NAKE YA FI SU A GIRMAN DARAJA BA.
Abinda ke faruwa ko ya faru ga mutum ne ke sa ayi wata magana a kansa wacce ,ke fito da darajarsa ko kuma qasqancinsa sakamakon ayyukansa, ko kuma abinda ya fari a kansa na cutarwa .
An kashe Annabawa (A.S )da yawa, kuma an cutar da wasu daga cikinsu, amma abinda ya faru a kansu (A.S )na cutarwa bai kai abinda ya faru kan Manzon Allah (S.A.W.W )ba. Saboda haka Manzon Allah (S )ya fi kowa daraja, amma wannan daraja tasa ba ta gana ya fi su cutuwa kan hanyar Allah ba.
A'imma (A.S )ma sun sami kansu cikin irin wannan cutarwa, domin an shayar da wasu guba (poison )daga cikinsu wanda hakan,yayi sanadin shahadarsu. Wasu kuma anyi musu kisan gilla kamar dai yadda aka yiwa Annabawa (A.S ).
Idan mu kayi nazari kan abinda ya faru ga Annabawa da A'imma (A.S ), sannan muka auna shi da abinda ke faruwa ga Sayyid (H )za mu san cewa lalle Allah ya jarraba shi fiye da yadda ya jarraba manyan bayinsa Manzanni (A.S ).
Duk wani nau'in cutarwa da aka yi musu, to, an yiwa Sayyid (H ). Bari na ba ku misali don sauqaqa muku wajen fahintar wannan magana tawa.
Daga cikinsu akwai:-
-An fadi miyagun kalmomi a kansa cewa shi kafiri ne dan ta'adda.
-Ya sha duka kan wannan kira nasa.
-An zubar masa da jini.
-An shayar da shi guba.
-An sanya shi ciki, gidan yari (prison ).
Idan muka nazarci wadannan misalai za muga cewa ko da ya yi tarayya da wasu cikin nau'o'in cutarwar, to, shi ya fisu dadewa cikin gidan yari (prison ).
Qari akan wannan shine , bayan kashe shi da Sojoji su kayi a Zaria 2015, Allah ya rayar da shi, sannan aka cigaba da yi masa sabuwar jarrabawa kan wacce aka yi mata ta baya.
Wannan sabuwar jarrabawar ita ce, cigaba da tsare shi cikin munanan raunuka (wounds ).
Tare da A.I.G
~17th January , 2020.
Tags:
Jagoran Gaskiya