Jana'izar Shaheed Qassem Sulaimani, tamkar jefa kuri'a ne tsakanin gaskiya da karya a duniya.




-Sakon sabon magajin Qassem Sulaimani, Manjo Janar Esma'il Gha'ani zuwa ga Qa'id jagora Sayyid Ali Khamnei (DZS)

Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.

Shahadar Laftana Janar Qassem Sulaimani,da kuma miliyoyin mutanen da muka gani yayin shahadarsa da kuma jqn'izarsa wadanda suka fito domin nuna alhininsu kan kisan nasa,tare da yin Allah wadarai ga Amurka da yan kanzaginta ya nuna cewar,hanyar Qassem Sulaimani ita ce mafita,kuma ita ce mutane suka jefa wa kuri'arsu inji Janar Gha'ani.
-
Ya jagoranmu,kuma abin kaunarmu.
 Ina mai yi maka ta'aziyar shahadar wannan babban gwarzo namu wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yakar ta'addanci da yan ta'adda 'wato 'Laftana Janar Qassem Sulaimani. Sannan ina yi maka ta'aziyyar shahadar abokin aikinsa Injiniya Abu Mahdi da sauran yan rakiyarsu.
-
Ya jagornmu (mai hangen nesa)
Ina mai tabbatar maka cewar,kamar yadda muka yi maka arkawarin daukar fansa kan Amurka,to lallai mun fara da kai musu hari kan sansaninsu mafi girma a cikin Iraqi,kuma mun yi nasara wajen kai wannan harin.
Kuma harin ya dace da hukuncin majilasar Iraqi na wacce tayi sokar cewar,basa kaunar zaman Amurka a kasar tasu.
-
Ya jagora !
Zan sake yin amfani da wannan damar domin nuna godiya ta gareka bisa zabata da kayi a matsayin sabon magajin gwarzon kwamandarmu Shaheed Qassem Sulaimani,domin na jagoranci wannan runduna mai muhinmanci wanda Janar Sulaimani ya yi shahada a cikinta.
Ina mai tabbatar maka cewar,babu abin da ya tsaya tun daga ranar shahadar tasa a wannan rundunar,kuma da yardar Allah zamu cigaba daga inda Shaheed Qassem  Sulaimani ya tsaya har zuwa numfashinmu na karshe.
-
Ya jagora !
Mun ga cincirindon al'umma wajen nuna alhininsu da kuma tsine wa Amurka yayin jan'izar wannan babban gwarzon namu (Shaheed Qassem Sulaimani) yayin gabatar da jana'izarsa.

Wannan tamkar yin zaben jin ra'ayin mutane ne tsakanin gaskiya (gwagwarmaya) da kuma karya (Amurka)
Don haka tafarkin Shaheed Qassem Sulaimani ne ya samu gagarumin rinjaye.
Don haka akan haka zamu dora har zuwa nasara da yardar Allah.
-
Amincin Allah ya tabbata ga Shaheed Qassem Sulaimani abokin aikinmu.

Nasir Isa Ali

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post