
Daga Wakilin Shafin Mu --Idishia Jos.
Cikin khudubar sallar juma’a da jagoran juyin-juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gabatar, irinta ta farko cikin shekaru 8, shugaban addinin ya gargadi al’ummar kasar kan yaudarar da Amurka ke shirin yi musu wajen yi musu dadin baki a wani yunkuri na ganin ta tunzurasu sun juya baya ga gwamnatin kasar.
Cikin khudubar ta Khamnei wadda itace irinta ta farko da jagoran na Shi’a ya gudanar cikin shekaru 8, ya nanata cewa dambarwar kuskuren kakkabo jirgin Ukraine dauke da fasinja 176 bata isa ta shafe batun daukar fansarsu kan Amurka game da kisan Soleimani ba.
A cewar Khamnei, wanda rabonsa da hawa mambarin khudubar juma’a tun a shekarar 2012, ya ce wasu makiya na amfanin da batun kuskuren kakkabo jirgin wajen tunzura al’ummar Iran don su juya baya ga gwamnati tare da hadawa Iran tarnaki ta cikin gida.
Khamenei wanda ya bayyana kuskuren kakkabo jirgin na Ukraine a matsayin babban abin takaici kawo yanzu ya ke ci gaba kuna a zuciyoyin al’ummar kasar da masoyanta, ya manyan makiyan Iran na son siyasantar da lamarin.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates