Ina Da Sharuda Huɗu Kafin Na Aurar Da Ɗana Ga Baturiya Inji Mahaifin Sulaiman!!!


🇨🇮Ma'asumah Nigerian News Update

_Mahaifin matashin da baturiya ta biyo Kano zai kai maganar gaban jami’an tsaro na ‘SSS’.

_Mahaifin matashin da baturiya ta biyo unguwar Panshekara dake jihar Kano, Malam Isa Sulaiman, yace zai kai maganar gaba jami’an tsaro na farin kaya wato State Security Service.



_Matashin ya hadu da masoyiyar tasa ne, Janine Sanchez a dandalin sada zumunta na Instagram a bara inda har magana tayi karfi mahaifiyar matashin ta amince ya auri baturiya Janine Sanchez.

_Rahoton Dabo FM ya bayyana cewa mahaifin matashin wanda tsohon dan sanda ne yace ya amince da auren amma fa sai an cika wasu sharuda guda 4!.

_A safiyar Asabar Malam Isa ya bayyana cewa “Tilas sai hukumomi sun bada umarnin yin hakan ba matsala bane, a matsayi na na tsohon jami’in tsaro ni nasan abinda nake fada, saboda hakan ma ranar litinin zan je naga shugaban jami’an tsaro na farin kaya.

_”Sharadi na 2 shine lallai a bar matashin ya karasa karatun sa idan sunje kasar Amurka.

_Sharadi na 3 shine Tilas ya zauna cikin addinin musulinci, Malam Isa ya kara da cewa “Duk da ita ma ta amince da hakan, watakil ita ma ta musulinta.

_”Na karshe shine dole Baturiya Janine Sanchez ta kawo rubutacciyar yarda daga iyaye ko waliyyinta saboda musulinci bai yarda mace ta aurar da kanta ba.

_Nan dai da sati kadan Janine Sanchez zata koma California dake kasar Amurka domin shirye shiryen dowowa bikin ta da masoyinta dan unguwar Panshekara a watan Maris. Kamar yadda KanoFocus ta fitar.

_Kubiyomu Ashiri nagama a madadin ma'aikatan ma'asumah nigerian news update tare dani mj matashi nakecewa a biyu mu a shiri nagaba


KUKASANCE DA MA'ASUMA NIGERIAN NEWS UPDATE
AKO  DA YAUSHE DOMIN ILIMAN TUWA DA SANIN YADDA DUNIYA KECIKI.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post